PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-07-27 (xsd:date)
?:headline
  • Lemon Zoɓo baya maganin zazzaɓi- aje asibiti (sw)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani rubutu da aka buga a Facebook yayi iƙirarin cewa lemon zoɓo na maganin zazzaɓi. Yadda ake lemon zoɓo na magani, rubutun ya fara. Ya bayyana yadda za ayi lemon da a fara jiƙa ganyen zoɓo, abarba, ganyen lemongiras, citta, biturut, lemon zaƙi, kankana da ruwa. Zoɓo dai wani lemo ne da ya shahara a Najeriya, wanda ake yi da busasshiyar filawar itacen rosilli. Itacen rosilli , wanda ake kira da habiscus sabdariffa a kimiyance ya fito ne daga ayarin itatuwan Malvaceae. Yana fitowa a wurare masu zafi, yana kuma da launin kore mai duhu ko jajayen kara da ganye. Shin lemon da aka bayyana a rubutun yana maganin zazzaɓi? Abubuwa da dama na jawo zazzaɓi Zazzaɓi shine ƙaruwar zafin jiki sama da maki 37 a ma’aunin selshiyos. Wanda ke nuna alamun shigar cuta, kamar yadda Mayo Clinic suka bayyana. Wasu daga cikin alamun zazzaɓi sun haɗa da ciwon kai, rawar jiki, rashin ɗanɗano, rashin ruwa a jiki da kuma kasala. Hukumar lafiya ta Britaniyya(NHS) tace abubuwa da cututtaka da dama na iya jawo zazzaɓi . Yana kuma daga cikin alamun cutar Covid-19. Mutane- manya da yara- idan zazzaɓi ya kama su tare da ciwon kai mai zafi, jijjiga, rikicewar tunani, yawan amai, ciwon ciki da wahala wajen numfashi, ana basu shawarar zuwa asibiti cikin gaggawa. Kada a ɗauki zazzaɓi akan abu mai sauƙi Wannan haɗin gargajiya ne, ayi watsi da shi, Cewar Marycelin Baba, Farfesa a fannin ƙwayoyin cuta ta jami’ar Maiduguri , kamar yadda ta shaidawa Africa Check. Baba wadda suka wallafa wata takarda akan gaza gane cutar zazzaɓin cizon sauro da zazzaɓin taifot. Babu wata hujja a kimiyance da ta goyi da bayan wannan da’awar, cewar Farfesar. Wannan haɗi baya magani ko hana zazzaɓi. Ƴaƴan itatuwan da aka lissafa na da muhimmanci a jiki amma ba maganin zazzaɓi ba ne. Baba ta ƙara da cewa: Idan an kamu da zazzaɓi, a hanzarta zuwa asibiti. Kada a dogara da haɗe-haɗe. Kada a ɗauki zazzaɓi da wasa (sw)
?:reviewRating
rdf:type
?:url