PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-04-07 (xsd:date)
?:headline
  • Tafarnuwa bata maganin chlamydia- ƙwayar cutar da ake yaɗawa ta hanyar jima’i, wadda zata iya jawo mummunar illa, don haka a je a sha magungunan da likita zai bayar. (sw)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Chlamydia cuta ce da ake yaɗata ta hanyar jima’i wadda ke kama maza da mata. Ƙwayar bakteriya chamdydia trachomatus ke haddasa ta, wadda idan ba’a yi maganin ta ba zata iya jawo matsala a lafiyar jiki nan gaba. Amma wani saƙo da aka wallafa a wani shafin Facebook a Najeriya da ke tallata magungunan gargajiya , yayi iƙirarin cewa cin tafarnuwa kafin a ci komai zai magance chlamydia. Saƙon na cewa : A ci tafarnuwa guda 2 zuwa 4 da safe kafin a ci komai na tsahon wata 1, sai a je ayi gwaji don tabbatar cewa babu cutar chlamydia. Wannan magani na da matuƙar inganci. Shin wannan maganin zai yi maganin chlamydia? Mun bincika. Ya zaku san kuna ɗauke da chlamydia? A cewar asibiti mallakar Amurka, wato Mayo Clinic , alamun cewa ana ɗauke da ƙwayar cutar Chlamydia trachomatus , sun haɗa da: Fitsari mai zafi Fitar ruwa daga gaban mace Fitar ruwa daga azzakarin namiji Jin zafi yayin saduwa ga mata Zubar jini tsakanin al’ada da kuma lokacin saduwa Zafi a ƴa’ƴan maraina ga maza Idan cutar ta daɗe zata jawo matsalar da zata dawwama. Cutar chlamydia tana shafar idanu, har ta kan jawo makanta, tana kuma illata hanyoyin fitar fitsari, idan ba’ayi maganin ta akan lokaci ba, Ademola Popoola , babban malami kuma ƙwararren likitan mafitsara, ya shaidawa Africa Check. Maganin cutar cikin sauƙi da magunguna masu kashe ƙwayar bakteriya Babban magani shine shan magungunan kashe ƙwayar cutar bakteriya, Popoola ya ƙara. Hukumar kiwon lafiya ta Britaniya ta bada shawara makamanciyar wannan. Za’a iya maganin Chlamydia da magungunan kashe ƙwayar cutar bakteriya, shawarar su akan cututtaka ta ambata . Ana buƙatar masu ɗauke da cutar da su ƙauracewa saduwa na tsahon kwanaki bakwai bayan an fara shan magani, don taƙaita yaɗuwar cutar. Dole a sha duk magungunan da aka buƙaci mutum ya sha don samun waraka daga cutar. Cin tafarnuwa kafin a ci komai bai zai warkar da cutar chlamydia ba. A je a ga likita. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url