PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2023-01-11 (xsd:date)
?:headline
  • Tsohon shugaban ƙasar Najeriya a mulkin soja Babangida bai wallafa goyan bayan Obasanjo na tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa Obi a shafin Tiwita ba (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • A TAƘAICE: Wani saƙon Tiwita da ke ta yawo a Facebook na cewa tsohon shugaban ƙasar Najeriya a mulki soja Ibrahim Babangida ya ce, ya girmama tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo bisa tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar Labour Peter Obi. Sai dai saƙon ya fito ne daga wani shafin Tiwita na bogi. Janar Olusegun Obasanjo zai kasance dattijon kirki na har abada kuma shugaban sojoji, a cewar wani saƙon Tiwita da aka wallafa a ranar 3 ga watan Janairun 2023. Babu wani soja da ke kan aiki da ya shiga aikin soja kafin shekarar 1982. Inda a lokacin Obasanjo tuni ya gama aikin soja. Ina girmama shi sosai akan abun da ya tsayar. Saƙon na Tiwita ya fito ne daga wani asusun shafin Tiwita mai suna Ibrahim B. Babangida wanda ke amfani da sunan @General_Ibbro. Ibrahim Babangida tsohon shugaban sojoji ne wanda kuma tsohon shugaban ƙasar Najeriya ne da yayi mulki a shekarar 1985 zuwa 1993. Olusegun Obasanjo shugaban ƙasar Najeriya ne daga shekarar 1999 zuwa 2007, kuma ya kasance mai faɗa aji a harkokin siyasar ƙasar. A ranar 1 ga watan Janairu ya tsayar da Peter Obi daga jam’iyyar Labour a matsayin ɗan takarar sa na shugaban ƙasa a zaɓen ƙasar mai zuwa, wanda za’ayi ranar 25 ga watan Fabrairu. An wallafa hoton allon waya da aka dauka na saƙon na Tiwita a Facebook a nan , nan , nan da nan . Da gaske Babangida ya aika saƙon na Tiwita, cewa yana girmama Obasanjo saboda tsayar da Obi? Mun bincika. ‘Waɗanda suke da hannu wajen wallafa saƙon Tiwitan maƙaryata ne’ Bayanan da ke shafin @ General Ibbro na nuna shafin na bogi ne. Amma hakan bai hana mutane yin tsokaci da rarraba saƙon ba. A lokuta da dama Babangida ya fito ya sanar da cewa shi fa bashi da shafi a kafafen sada zumunta. A shekarar 2018, Babangida ya keɓe sanarwa cewar kafar sada zumunta ta Tiwita da ke amfani da sunansa, sunayi ne don a soke shi. Kassim Afegbua, mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasar ya ƙaryata da’awar da ke cewa Babangida ya tsayar da Obi. Ba gaskiya ba ne. Ayi watsi da rahoton cewa ya tsayar. IBB bashi da shafin Tiwita, kamar yadda ya shaidawa Nigerian Tribune . Idan ma har zai yi magana, zai yi ne ta sanarwar da ya sawa hannu bata Tiwita ba. Waɗanda ke da hannu wajen wallafa saƙon Tiwitan maƙaryata ne. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url