PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-03-05 (xsd:date)
?:headline
  • Haɗin zoɓorodo da ruwan ganyen rogo baya maganin cutar sikila (tl)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Haɗa zoɓorodo da ruwan ganyen rogo zai magance cutar sikila, wani saƙo da ke yawo a Facebook ya ce. Saƙon yayi bayanin yadda za’ayi haɗin da yadda za’a sha, inda aka ƙare rubutun da cewa, ayi wannan haɗin na tsahon watanni biyu. Cutar sikila , cuta ce da ake gado, ana samun matsala a ƴaƴan halittar jini. Ana samun hanyoyin ƙwayoyin halittar jan jini su rasa ikon buɗewa da tsukewa, ta haka suke toshe ƙananan hanyoyin jini, su kuma naƙasta gudanar jini. Hakan sai ya haifar da matsala wajen ƙarancin sinadarin oksijin a cikin jini. Cutar na haifar da matsalar oksijin a jiki, tsananin raɗadi a jiki, ƙwayoyin cuta na bakteriya da kuma mutuwar tsokar jiki. Shin haɗin zoɓorodo da ruwan ganyen rogo na maganin cutar? A ga likita don karɓar maganin da ya dace Cutar sikila tafi ƙamari a nahiyar Afrika, ana haihuwar jarirai sama da 300,000 da matsananciyar matsala a jinin su a kowacce shekara, a cewar Ƙungiyar Lafiya ta Duniya . Africa Check ta tuntuɓi Omolade Awodu, Farfesa a fanin lafiyar jini a jami’ar Benin da ke kudu maso yammacin Najeriya, don tambayar ta ko wannan haɗin da ake yaɗawa a Facebook na maganin cutar sikila. Ban taɓa cin karo da wani bincike da ya ce hakan ba, Farfesan ta ce. Baya cikin hanyoyin magance cutar sikila. Masu fana da cutar suje asibiti don ganin ƙwararru a fannin. Idan yara ne ƴan ƙasa da shekaru 16 su nemi likitocin da suka ƙware a fannin duba lafiyar yara, idan kuma manyan ne su nemi ƙwararru akan fannin jini. Awodu ta ce masu fama da cutar su tabbata suna kiyaye lokutan da likita ya buƙaci ganin su, kuma su yi amfani da shawarwarin da likitoci suka basu don kula da lafiyar su. Ta ƙara da cewa a yanzu akwai hanyoyin kula da masu ciwon da dama, waɗanda suka samu amincewar ƙwararrun masana magunguna. Cibiyar kiyaye yaɗuwar cututtuka ta Amurka ta bada hanyoyin da masu fama da cutar da iyalan su zasu ringa bi don gujewa tashin ciwon da kuma lokacin da ya kamata su ga likita. A wani rahoto akan cutar sikila a Najeriya , Africa Check ta gano cewa Najeriya ke da mafi yawan masu fama da cutar a duniya. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url