?:reviewBody
|
-
A TAƘAICE : A hoton da aka sauyawa kamanni, an nuna Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressive Congress kamar yana kallon ɗan jam’iyyar Labour Peter Obi, a cikin jirgin sama. Amma a hoton na ainihi, talabijin ɗin babu hoto a cikinta. Wani hoto da aka wallafa a Facebook na nuna Bola Tinubu ɗan takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 daga jam’iyyar All Progressive Congress , a cikin jirgin sama yana kallon abokin hamayyarsa Peter Obi a talabijin. Obi ɗan takara ne daga jam’iyyar Labour . Charles Oputa sanannen mawaki kuma ɗan wasan kwaikwayo a Najeriya, wanda akafi sani da Charly boy ne ya saka hoton a ranar 8 ga watan Oktoba 2022 a shafinsa na Facebook mai mabiya 13,000 . Barka da dawowa gida ɗan uwa. Wannan shine mutumin da ya kamata a kalla, taken da ya sawa hoton kenan. Ƴan Najeriya zasu zaɓi sabon shugaban ƙasa a ranar 25 ga watan Fabrairu a shekarar 2023 . Da gaske hoton ya nuna Tinubu yana kallon Obi a talabijin yayin da ya ke tafiya a cikin jirgin sama? Mun bincika. Tinubu na kallo tagar jirgi Bincike da kafar bincikar hoto ta Google reverse image search ya tabbatar da cewa hoton an sauya shi. Binciken ya nuna cewa an ɗauki hoton a farkon watan Oktoba yayin da Tinubu ke dawowa Najeriya daga Biritaniya. An ganshi da irin kayan da ke jikin sa a hoton a wasu hotunan na sa. Ainihin hoton , wanda taron magoya bayan sa suka saka a Tiwita a ranar 6 ga watan Oktoba- kwanaki biyu kafin Oputa ya saka a Facebook- Tinubu na kallon taga ne a cikin jirgi. Talabijin ɗin da ke gaban sa ma allonta babu hoto a ciki. Wani labaran da aka fitar akan dawowar ta sa Najeriya, na haɗe da hoton na ainihi da wasu hotunan da aka fitar wajen bikin murnar dawowarsa.
(id)
|