PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-04-29 (xsd:date)
?:headline
  • Babban jami’in bankin cigaban Afrika bai nuna goyan bayan sa ga wani mai son zama shugaban ƙasa ba (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Dimbin saƙonni a Facebook na iƙirarin cewa shugaban bankin cigaban Afrika , Akinwunmi Adesina, ya nuna goyan bayan sa ga Bola Tinubu, ɗaya daga cikin dinbim ƴan siyasar da ke son su gaji kujerar shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2023. Saƙonnin waɗanda aka wallafa su a watan Afrilun 2022, sun yi iƙirarin cewa Adesina ya ce: Matuƙar sanata Bola Ahmed Tinubu zai iya saka Legas ta zama ta 5 cikin garuwa masu yawan tattalin arziki a Afrika kuma jiha mafi tsaro a Najeriya, wannan ya tabbatar da abun da zai iya yi. Tinubu yayi gwamnan jihar Legas daga shekarar 1999 zuwa 2007, ya kuma cigaba da zama ɗan siyasa mai faɗa a ji a jihar da jami’iyyar All Progressive Congress . Bayan wata ganawa da Buhari a ranar 10 ga watan Junairun 2022, Tinubu ya bayyana aniyarsa ta son takarar kujerar shugaban cin Najeriya a zaɓen 2023. Amma Adesina, wanda yayi ministan noma a Najeriya daga shekarar 2011 zuwa 2015 ya goyi bayan tsayawar Tinubu takarar shugaban ƙasa? Ofishin Adesina sun ƙaryata da’awar An fara yaɗa da’awar a yanar gizo a watan Janairun 2022 , jim kaɗan bayan Tinubu ya bayyana aniyarsa ta son yin takarar shugaban ƙasa. Tun lokacin Adesina ya ƙaryata da’awar . Jaridar Guardian ta ruwaito a ranar 12 ga watan Janairu cewa babban mai bawa Adesina shawara akan sadarwa Victor Oladokun ya ce da’awar ƙarya ce, ɓarna ce kuma zamba ce. Oladokun ya ce Adesina bai nuna goyan bayansa ga kowa ba. Sai dai kuma, magoya bayan Tinubu na cigaba da yaɗa da’awar a Facebook. Da’awar ƙarya ce. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url