PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-06-24 (xsd:date)
?:headline
  • Babu hujjar cewa sojojin Najeriya 300 sun bar aiki tun bayan hatsarin jirgin saman da yayi sanadin mutuwar shugaban sojojin (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • SAMA DA SOJOJIN NAJERIYA 300 NE SUKA BAR AIKI BAYAN JIRGIN DA AKE ZARGI YA FADO DA SHUGABAN SOJOJIN DA WASU, cewar wani rubutu da aka wallafa a Facebook a Najeriya, a watan Mayu 2021. Rubutun ya ƙara da cewa: MU DAI MUNA ZUBA IDO. Lt Gen Ibrahim Attahiru , shugaban sojoji, ya rasa ransa da wasu mutane 10 ranar 21 ga watan May u a wani hatsarin jirgin sama a jihar Kaduna, arewa maso yammacin Najeriya. Jirgin ya taso ne daga Abuja, babban birnin tarayya, inda ya faɗi yayin da ya ke ƙoƙarin sauka a Kaduna sanadiyar rashin kyan yanayi. Ko sojojin Najeriya da dama sun bar aiki bayan afkuwar hatsarin? Mun bincika. Bamu samu inda aka fitar da labarin cewa sojoji 300 sun bar aiki ba Labarin barin aikin sojoji na kwana-kwanan nan dai anyi shi tun watan Junerun 2021, inda aka ce an bawa sojojin 127 damar ajiye aiki idan suna so kafin watan Mayu. Kwamitin wakilai a Najeriya ya tabbatar da cewa a bayan watanni hudu na shekarar 2020 dai sojoji 386 sun ajiye aikin da kansu , dalilin matsalar rashin lafiya da wasu matsalolin. Amma babu rahoton barin aikin sojoji 300 bayan rasuwar Attahiru. Bamu samu shelar barin sojoji aiki ba a shafin rundunar sojojin, hanyoyin watsa labaran su ko a shafukan su na yanar gizo . (sw)
?:reviewRating
rdf:type
?:url