PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-09-06 (xsd:date)
?:headline
  • Har yanzu babu maganin warkar da ciwon HIV (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani saƙo da ke yawo a Facebook a ƙarshen watan Junin 2021 na iƙirarin cewa yanzu an samu maganin warkar da ciwon HIV. Saƙon yace , kawai; Maganin warkar da HIV ya fito. Bai yi wani ƙarin bayani ba ko faɗar tushen bayanin ba. Ƙwayar cuta mai karya garkuwar jiki , ko HIV, na kaiwa fararen ƙwayoyin halittar jini hari , musamman ƙwayoyin halitta na CD4, sai su raunana garkuwar jiki. Ana yaɗata ta hanyar haɗuwar jinin mai cutar dana mai lafiya ko haɗuwar ruwan jiki, lokacin saduwar jima’i ko daga uwa zuwa ɗa yayin haihuwa ko shayarwa. A shekarar 2020, ƙasar Afrika ta Kudu na da ƙiyasin masu ɗauke da cutar har mutane miliyan 7.8 . Wanda ya ɗan haura kashi 13% na jama’ar ƙasar. Cutar ƙarancin adadin ƙwayoyin halitta masu garkuwa daga cututtuka a jiki, ko AID, ita ake nufin da mafi tsananin cutar HIV . Sai dai kuma da amfani da magungunan da akafi sani da antiritorobairal terap i ko ART, masu fama da cutar HIV basa kaiwa matakin da cutar zata zama AIDS. Amma an samu maganin warkar da cutar HIV? Mun bincika. ‘Babu sahihin maganin warkar da HIV’- CDC A cewar hukumar kiyaye yaɗuwar cututtaka ta Amurka, ko CDC, a halin yanzu babu wani sahihin maganin warkar da HIV. Za’a iya kula da HIV ta hanyar amfani da magungunan ART, waɗanda suka kasance haɗin magunguna ne da za’a ringa sha kullum. Waɗannan magunguna zasu rage yawan HIV a jiki, wato bairal lod, su kuma ƙara yawan CD4. Wannan na bawa jiki damar samar da garkuwar jiki don yaƙi da ƙwayoyin cuta. Ya rage yiwuwar yaɗa cutar ga wasu. Lokacin da ba’a samu samuwar ƙwayar cutar ba, ba za’a iya yaɗa ƙwayar cutar HIV ga abokan zama ta hanyar yin jima’i ba tare da amfani da abun kariya ba, hakan ma zai kiyaye yaɗuwar cutar daga uwa zuwa ɗa. Gwamnatin Afrika ta Kudu ta na bada ARTs ga masu ɗauke da cutar HIV tun 2003. Amma ART baya warkar da HIV. An yi gwajin alluran rigakafin HIV, amma ba’a amince da su ba tukunna Kamfanonin haɗa magunguna na Moderna da na Johnson & Johnson sun bayyana waɗanda za suyi gwajin alluran rigakafin cutar HIV da su. Moderna sun bayyana a ranar 18 ga watan Agusta 2021 cewa sun shirya don gwajin allurar rigakafin HIV akan yan adam. Sun yi amfani da fasahar mRNA irin wadda akayi amfani da ita wajen yin allurar rigakafin Covid-19. Johnson & Johnson sun kammala matakai biyu na gwajin waɗanda za’a yiwa allurar rigakafin a watan Agusta na 2021. An yi gwajin a ƙasashen Afrika na cikin hamada a kan mata waɗanda suke cikin barazanar ɗaukar ƙwayar cutar amma allurar rigakafin bata samar da isassiyar kariya daga ƙwayar cutar HIV ba. A halin yanzu babu allurar rigakafin HIV. Sannan allurar rugakafi zata kiyaye ɗaukar cutar ne ba zata warkar da cutar ba. (sw)
?:reviewRating
rdf:type
?:url