PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-05-27 (xsd:date)
?:headline
  • Kashi ‘90%’na ƙaton ciki ba ya nufin’ alamu ne na ciwon hanta- ana buƙatar cikakken bincike (sw)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Alamu na farko ga kitsen hanta ko hantar da ta kumbura shi ne potty belle, abun da wani saƙo da aka saka a Facebook Najeriya ke cewa. Yana nufin ƙaton ciki. Ƙaton ciki na nufin ciki zagayayye. Amma saƙo n na cewa masu ƙaton ciki na da kaso 90% na yiwuwar iya kamuwa da cututtukan kitse da na kumburin- hanta. Matuƙar kana da ƙaton ciki kana da kashi 90% na yiwuwar samun kitsen hanta, saƙon ya ce. Da gaske masu ƙaton ciki na da kashi 90% na yiwuwar kamuwa da cutar kitsen hanta? Mun bincika. Ciwon hanta na buƙatar gwaje-gwaje kafin a tabbatar da kamuwa da shi Kitsen hanta na nufin taruwar kitse a jikin hanta. Hanta itace sashen cikin jiki ma fi girma. ( Fata itace sashen jiki mafi girma, amma ita a wajen jiki take ba a ciki ba.) Hanta na daga gaban ciki daga ƙasan huhu, amma a saman tumbi. Abun da ake kira da ciki, na can ƙasa ƙarƙashen hanta da tumbi. Ciwon kitsen hanta ba shi da alaƙa da yawan shan barasa, ana kuma kiran sa da ciwon kitsen hanta wanda bashi da alaƙa da barasa . Yayin da kuma ciwon kitsen hanta wanda barasa ke jawowa , kamar sunan sa yawan shan barasa ke haddasa shi. Sauran cututtukan da kan iya jawo ciwon hanta su ne ciwon suga nau’i na biyu, matsananciyar ƙiba, ciwon hawan jini da hauhawar kitse a jiki. Dr Joanah Ikoba wadda babbar likitar yara ce da ta ƙware akan cututtukan cikin ciki da cututtukan jini kuma babbar malama a jami’ar Najeriya da ke Calabar , ta shaidawa Africa Check cewa girman ciki ba hanya ce ta tabbatar da kamuwa da kitsen hanta ba ko sauran cututtukan hanta ba. Ikobah ta ce ana gane ciwon hanta bayan anyi gwaje-gwaje masu dama, waɗanda suka haɗa da yin hoton sautin ciki wato ultrasound a ciki da gwaje-gwajen jini da kuma hoton sautin ciki na faibirosikan . Sauran gwaje-gwajen sun haɗa da gwajin da ake ɗaukar tsoka wato biopsy na hanta da kuma ɗaukar hoton ciki don bincike wato MRE . Ba dai-dai bane ace mutum yana da kitsen hanta ko wani ciwo da ya danganci hanta don kawai mutum nada ƙaton ciki, Ikobah ta shaida mana. Duk da cewa matsananciyar ƙiba na iya jawo kitsen hanta, amma marasa ƙiba za’a iya gano suna da ita. Ta ƙara da cewa maganin kowanne irin ciwon hanta ya danganta da abun da bincike ya nuna. Hanta mai kitse da wadda ta kumbura ana iya gano su ne kawai ta hanyar dubawa da kuma gwaje-gwaje. Ba lalle ne mutune masu ƙaton ciki ya zama suna da ciwon hanta ba. Haka nan mutanen da basu da ƙaton ciki zasu iya samun ciwon hanta. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url