PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-07-20 (xsd:date)
?:headline
  • Najeriya bata kirkiri takardun kuɗi na n5,000 da n2,000 ba (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani bidiyo da aka fitar a Facebook a watan Yulin shekarar 2021 ya nuna tulin abun da yayi kama da takardun nairorin Najeriya. An ɗaga hannu cike da nairori ga kemarar da ke ɗaukar hoton, waɗanda ke ɗauke da alama da sunan babban bankin Najeriya kuma takardun naira N5,000 da na N2,000. Ana kuma iya jin muryar mace. Haka kuɗin ya ke na takardun N5,000. Ya ce naira miliyan 17 ne.... ya ce wai shi mara hankali ne. Ya ce wai naira miliyan N18 ne, amma mun kirga. Naira miliyan N17 ne. Rubutun da ke ƙasan bidiyon na cewa : Yanzu muna da takardun naira na 5000 da 2000. Nawao. Jama’a sun kalli bidiyon sama da sau 34,000. Najeriya na fuskatar hauhawar farashin abubuwa da ƙarancin kuɗi a wannan lokacin. Shin da gaske gwamnatin tarayyar ƙasar ta ƙirƙiri sababbin nairorin N2,000 da N5,000? ‘Ƙarya ne kuma bogi ne’ Kafar tantance hoto ta reverse image search tayi amfani da fraim na bidiyon ta kai mu ga wani labari da aka buga shi a watan Junairun 2020 a shafin yanar gizo na Oriental Times . Shafin ya nuna bidiyon dai, tare da cewa wani mutum ya ziyarci banki a wani sashe na Najeriya da ba’a bayyana ba, ya saka kuɗade har naira miliyan N17 na takardun N5,000 da na N2,000. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url