PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-07-22 (xsd:date)
?:headline
  • Babu hujjar da ta tabbatar da cewa ɗan siyasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa Bola Tinubu yace ba zai halarchi muhawara akan shugabancin ƙasa ba saboda dalilin rashin lafiya (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani rubutu da aka wallafa a Facebook a Najeriya na iƙirarin cewa Bola Tinubu ya ce ba zai halarchi muhawara akan shugabancin ƙasa ba wadda gidan jaridan CNN International suka shirya, dalilin rashin lafiya. Tinubu shine ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar All Progressive Congress a babban zaɓen Najeriya da za’ayi a shekarar 2023. Rubutun da aka buga a ranar 15 ga watan Yulin 2022 ya ce : Bana jin daɗi, ba zan je muhawara akan shugabancin ƙasa ta CNN ba- Tinubu ya yi watsi da muhawara akan shugabancin ƙasa ta CNN. Mun ci karo da da’awowi makamantan wannan a Facebook a nan , nan da nan . Bola Tinubu ya faɗi hakan? Mun bincika. Babu shaidar yayi wannan magana Rubutun na Facebook bai bayyana waje da lokacin da Tinubu ya furta wannan magana ba. Binciken da akayi a sahihin shafin Tinubu na kafar sada zumunta ta Twita da kuma shafinsa na yanar gizo ba a ga inda yayi wannan magana ba. Haka nan babu rahoton yayi wannan magana a sahihan gidajen jaridu na gida dana wajen ƙasar, wanda tilas a samu rahoto daga gidan jarida idan da ya faɗi hakan. CNN bata shirya muhawarar shugabancin ƙasar ba tun lokacin da suka fara aiki a ƙasar a shekarar 2016 CNN ta buɗe babban wajen gudanar da ayyuka a Legas, Najeriya a shekarar 2016, amma basu gudanar da muhawarar shugabancin ƙasar ba ga ƴan takarar shugabancin ƙasar ba har kawo lokacin haɗa wannan rubutu. Bincike a shafin CNN na yanar gizo da shafin su na Twita akan wannan muhawara bai sa anci karo da wani abu makamancin sa ba. Ana kuma gudanar da muhawarar zaɓe ne a cikin muhallin yaƙin neman zaɓen ne kamar yadda hukumar zaɓe mai zamankanta ta ƙasa ta tanada. A hukumance za’a fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisa a ranar 28 ga watan Satumba 2022 zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu 2023. Da a ce CNN ta shirya muhawarar shugabancin ƙasar Najeriya, da zai kasance kafafen yaɗa labarai na gida dana waje sun yaɗata matuƙa. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url