PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-05-13 (xsd:date)
?:headline
  • Gargaɗi akan zamba! Ayi hattara da ‘tayin asusun tallafawa matasa na ƙasa a WhatsApp da Facebook Najeriya’ na bogi (tl)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani saƙo da ke assasa wani shafin yanar gizo - mai kama da sabon shafi da ke da taken takardar neman tallafin asusun tallafawa matasa na ƙasa na shekarar 2022 ta fito na ta kewayawa a Facebook da WhatsApp a Najeriya. Takarar neman izinin tallafin asusun tallafawa matasa na ƙasa na shekarar 2022 na yanar gizo ya fito da hanya mafi sauƙi don yin rijista ga duk ƴan ƙasa masu kishin ƙasa, waɗanda ke neman taimako akan kasuwancin su ko karatun su, saƙon y a ce Shafin na taryar waɗanda suka kai ziyara shafin da babban take da ke cewa shirin tallafin matasa na shugaban ƙasa. Sannan shafin na ɗauke da alamar ƙasashen Afrika kamar Ghana, Kenya, Najeriya, Afrika ta Kudu da Uganda. Saƙon ya ce shirin tallafawa matasa na shugaban ƙasa (P-YES) na son ganin ya ƙirƙiri damar tallafawa matasa da shirye-shirye a ƙalla 774,000 ta hanyar tallafawa matasan kai tsaye a cikin shekaru biyu. P-YES wani shiri ne na haɗin gwiwa tsakanin masu zaman kansu da gwamnati wanda ofishin mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa akan harkokin matasa da dalibai ke yi. Shafin nada takardar cike gurbi, inda mutane zasu iya cikewa don samun tallafi. Amma shafin- da asusun tallafawa matasan -na gaskiya ne? Ko dai masu neman masu zirga-zirga a shafi ne kamar yadda aka saba Kwanan watan shafin ya nuna an yi rijistar shafin a ranar 5 ga watan Afrilu 2022 da karfe 19:09. Bayan cike takarda neman izini, shafin na umartar waɗanda suka cike da su raba saƙon da abokai 5 ko a guruf na WhatsApp guda 5. Wannan ba tantama dabara ce ta neman masu ziyartar shafi, ire-iren waɗanda Africa Check ta zayyano muku a baya. ‘Masu zamba da suka ɓoye fuskokinsu Ranar 5 ga watan Fabrairu, P-YES sun wallafa gargaɗi ga masu neman gurbin da suyi amfani da shafin shirin tallafawa matasa na gaskiya . Ofishin babban mataimaki na musamman na shugaban ƙasa akan alamuran matasa da dalibai sun fahimci masu damfara da ke boye kawunansu na ƙoƙarin ganin sun damfari matasan Najeriya da jama’ar gari ta hanyoyi daban-daban wanda ta kai da sun haɗa da ofishin shirin P-YES, gargaɗin ya ce . Bincike ya nuna hanyoyin da suke bi sun haɗa da; masu damfarar na iƙirarin biyan tallafi ga matasan Najeriya ta hanyar umartar su zuwa shafukan yanar gizo na bogi, abun da ke ta yaɗuwa yanzu a kafafen sada zumunta na yanar gizo. Shirin P-YES ya nesanta kansa da masu alaƙa da su daga waɗannan mazambata. Africa Check ta ƙaryata zambar yanar gizo da ke tallan aikin yi, bada tallafi, bashi da kyaututtuka. Ku karanta wannan don sanin hanyoyin gano su . (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url