PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-12-13 (xsd:date)
?:headline
  • Tsohon gwamnan jihar Lagos Tinubu bai nuna sha’awar zama shugaban ƙasa ba (sw)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Ubangiji ne kawai zai iya hana ni zama shugaban ƙasa- Tinubu, a cewar wani rubutu a Facebook da aka wallafa a ranar 4 ga Disemba 2021. Asiwaju Bola Tinubu, jagorar jam’iyyar All Progressive Congress (APC) na ƙasa, ya ce yana sane da cewa ƴan Najeriya a fusace suke bisa gazawar masu mulkin ƙasar, da kuma gazawar gwamnatin ƙasar wajen ka sa inganta rayuwar ƴan ƙasar. Tinubu dai tsohon gwamnan jihar Lagos ne da ta ke kudu masu yammacin Najeriya kuma tsohon ɗan majalisar dattawa ne. Tun dai bayan ya bar muƙaminsa ya ke ta harkar siyasa, inda ya ke wa jam’iyyar APC yaƙin neman a zaɓe ta , a matsayinsa na jagorar jam’iyyar All Progressive Congress na ƙasa. Amma Tinubun ya faɗi waɗannan kalamai? Babu hujjar da ta tabbatar da Tinubun ya faɗi hakan Rubutun bai nuna waje da lokacin da Tinubun ya faɗi hakan ba. Irin waɗannan kalamai idan dai har an faɗe su suna kasancewa kanun labarai a duk kafafen watsa labaran Najeriya. Sai dai babu wata ingantacciyar kafar watsa labarai da ta ruwaito hakan. Duk da cewa akwai ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓe da suke nuna goyan bayan su ga ɗan siyasar, amma dai bai taɓa magana akan hakan ba ko bayyana sha'awarsa na neman wata kujerar mulki. Saƙon na ƙarya ne. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url