?:reviewBody
|
-
FG TA AMINCE DA ƘARIN KASHI 300% NA ALBASHIN MA'AIKATAN NIMC, wani saƙon da aka wallafa a Facebook a watan Satumba 2021 ke cewa. SU KUMA LIKITOCI DA MALAMAN JAMI’A FA? FG na nufin gwamnatin tarayyar Najeriya- wadda take daban daga gwamnatocin jihohin ƙasar guda 36 . Hukumar kula da shaidar ƴan ƙasa , ko NIMC, hukuma ce ƙarƙashin gwamnatin tarayya wadda ke da alhakin kula da bayanan shaidar tabbata ɗan ƙasa. An rarraba rubutun da dama, kuma masu tsokaci a ƙasan rubutun sun tambayi tushen labarin. Wani mai amfani da Facebook da yayi tsokaci ya ce : A ina aka samu kashi 300%? Labaran da ake samu a kafafen watsa labarai na cewa kashi 200% amma ku kuna ƙara adadin kuna cewa kashi 300% don ku rikitar da jama’a. Da gaske gwamnatin tarayya ta amince da ƙarin kashi 300% na albashin ma’aikatan hukumar? Mun bincika. Ƙari daga naira biliyan 5 zuwa naira biliyan 16.7 A watan Satumba, gwamnatin tarayya ta amince da sababbin dokokin aiki na ma’aikatan NIMC, waɗanda suka haɗa da gyaran albashi. A cewar ministan sadarwa da fasahar zamani , Isa Pantami, sababbin dokokin suka sa gaba ɗaya abun da ake biyan ma’aikatan gaba ɗayan su ya ƙaru da kashi 200%. Pantami ya ce kudin ya kasance naira biliyan 5 ne a shekara. Ƙarin yasa kuɗin albashin gaba ɗaya ma’aikatan ya kama naira biliyan 16.7 a shekara. Wannan ya zama ƙarin 234% - ba 300% ba.
(id)
|