?:reviewBody
|
-
Bidiyon jirgin da bashi da fuka-fukai akan hanya mai cike da ababen hawa ya yawata a kafafen sada zumunta a Najeriya, aka kuma yi iƙirarin cewa jirgin sama ne ya faɗo yayin da zai sauka akan titi kusa da tashar jiragen sama ta ƙasa da ƙasa ta Murtala Mohammed da ke Ikeja, Legas. An kuma wallafa da’awar a wasu shafukan watsa labarai a ƙarshen watan Mayu 2022. Amma meye gaskiyar labarin? Hukumomi sun ƙaryata da’awar Hukumar tashoshin jiragen sama ta tarayya (FAAN), hukumar gwamnati da ke da alhakin kula da tashoshin jiragen sama a ƙasar, ta ƙaryata da’awar. FAAN ta ce a ranar 24 ga watan Mayu a wani rubutu da suka wallafa a Facebook ga jama’a ayi watsi da labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an samu fadowar jirgi a tashar jirage ta Ikeja. Mamallakin jirgin ne ya sayar da jirgin, yana kuma ƙoƙarin kai jirgin inda aka saya. Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas ma ta ƙaryata da’awar, inda ta ce babu abun da ya faru, kamar yadda jaridar Punch ta wallafa. Babu alamun faɗuwar jirgi Jirgin da ke cikin bidiyon bai nuna alamun cewa faɗuwa yayi ba, sannan daga gani an cire fuka-fukan jirgin a tsanake. A wasu sakonnin Twita , wani mai nazari akan jiragen sama Daniel Dikio ya ce jirgin samfurin Airbus A319 ne, kuma an cire fuka-fukan sa ɗaya bayan ɗaya a tsanake. Hakan kuma ba zata faru ba idan jirgin faɗowa yayi, cire fuka-fukan na nuna alamun cewa ciccire kayan jirgin ake. Jikin jirgin bai ɓaci ba, wanda hakan ba zai taɓa yiwuwa ba idan da abun da ake zato ne na cewa jirgin faɗowa yayi. Nayi nazarin bayanan jirgin sama, ban samu wani abu na daban ba. Kuma duka jiragen A319 da ke aiki a Najeriya a lissafe suke a lissafin da nayi, Dikio ya rubuta a sakon na twita .
(sw)
|