PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-03-31 (xsd:date)
?:headline
  • Buhari bai cewa sojojin Najeriya suyi shirin yaƙi ba (sw)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani hoto da ke yawo a Facebook na nuna shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari yana cewa sojojin ƙasar da su yi shirin yaƙi. Hoton na yanayi da hoton da ake ɗauka na hoton allon waya wato sikirinshot na wani rubutun tiwita daga shafin @MBuhari, wanda shafi ne mallakin Buhari . Rubutun tiwitan na cewa: Muna tare da Ukraine a wannan mawuyacin hali, bayan magana da shugaba Biden akan irin tsare-tsarensa, na sanar da jami’an sojojina da suyi shirin yaƙi! Ba zamu bar wannan ya kuɓuce ba. A ranar 24 ga watan Fabrairu ne ƙasar Rasha ta mamaye maƙwabciyarta, ƙasar Ukraine, a lokacin kuma mummunan faɗan da ya ɓarke tsakanin su ya zama kanun labaran da aka fi yaɗawa a duk faɗin duniya. Shin da gaske Buhari yayi wannan rubutun a shafinsa na tiwita, wato cewar, ya sa sojojin ƙasar cikin shirin ko ta kwana, bayan ya zanta da shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ? Mun bincika. Babu hujjar da ta tabbatar da sanarwar A sahihin shafin Buhari na tiwita rubutu na ƙarshe da akayi an yi shi ne a ranar 1 ga watan Yunin 2021, kwanaki kaɗan kafin gwamnatin tarayya ta haramta amfani da shafin tiwita a ƙasar. An ɗage haramcin amfani da shafin a ranar 12 ga watan Janairu 2022, amma shugaban ƙasar baiyi rubutu a shafin sa ba bayan ɗagewar. Wata alamar da ta nuna cewa hoton allon wayar na bogi ne, shi ne yawan kurakuren da ke cikin rubutu, wanda abu ne mawuyaci ace daga ofishin shugaban ƙasa saƙon ya fito. Babu kuma wata kafar yaɗa labarai a Najeriya da ta fitar da labarin. Duk hujjoji sun tabbatar da cewa ƙirƙirar labarin akayi. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url