?:reviewBody
|
-
A taƙaice : An danganta wasu maganganun waɗanda ke kai farmaki ga Omoyele Soworo na jam’iyyar African Action Congress, waɗanda ke cewa ya ce zai ɗaure shugaban ƙasar Najeriya Buhari. Sai dai babu wata hujjar da ta tabbatar da cewa Soworo ya faɗi wani abu makamancin hakan. Wani saƙo a Facebook da ke ta yawo a Najeriya na cewa Omoyele Soworo ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar African Action Congress (AAC), na cewa Zan ɗaure Buhari idan na zama shugaban ƙasa a 2023. Sowore mai fafutukar kare hakkin bil adama ne a Najeriya, mai yaƙin ganin cigaban demokaraɗiya kuma mamallakin gidan jaridar yanar gizo ta Sahara Reporters . A zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019 , Soworo a ƙarƙashin tutar AAC, ya fito adawa da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Sai dai ya tashi da kuri’u 33,953 daga cikin kuri’u 28,614, 190 da aka kaɗa, yayin da Buhari ya lashe da kuri’u 15, 191, 847. A watan Agustan 2019, an kama kuma an tsare Soworo dalilin haɗa zanga-zangar #RevolutionNow . An kuma tuhume shi da laifin cin amanar ƙasa kafin a sake shi a ranar 24 ga watan Disemba. Gwamnati ta ƙara tuhumar Soworo da laifin shirya makircin cin amanar ƙasa da zagin Buhari a wata tattaunawa. Da’awar 5 ga watan Satumba wadda ta kawo kalaman Soworo na cewa zai ɗaure Buhari, an sake maimaitata a wasu saƙonnin Facebook. Sowore ya faɗi waɗannan kalamai, waɗanda ka iya sawa a sa ke tsare shi? Mun bincika. Babu hujjar da ta tabbatar da waɗannan kalamai Ainihin saƙon bai bayyana waje da lokacin da Soworo ya faɗi kalaman ba. Wannan alamun tambaya ne, waɗanda ke tabbatar da cewa ƙirƙirar da’awar da ke yawo a kafafen sada zumunta akayi. Babu wani rahoto a manyan gidajen jarida na cewar Soworo ya furta waɗannan kalamai, ko wani abu mai kama da son ɗaure Buhari. Idan akayi la’akari da tarihin Soworo, irin waɗannan kalamai dole ne a sa me su a rahotonnin ingantattun gidajen jarida. Mun kuma binciki sahihin shafin Soworo na Tiwita , amma ba mu samu wani abu makamancin waɗannan kalamai ba. Africa Check na cigaba da samun ƙaruwar kalamai da tsokaci ire-iren waɗannan da ake dangantasu ga manyan ƴan siyasa, yayin gabatowar zaɓen Najeriya na 2023. Irin waɗannan kalaman ƙarya zasu iya gurɓata muhawarar siyasa a yanar gizo. Waɗannan kalamai da aka ƙirƙira aka dangantasu ga jam’iyyar adawa ɗaya ne daga cikin misalan hakan.
(id)
|