PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-10-28 (xsd:date)
?:headline
  • A kiyayi damfara- babban bankin Najeriya baya bada kuɗin eNaira na biliyan 50 (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani rubutu da ke yawo a WhatsApp da Facebook a Najeriya na iƙirarin cewa babban bankin ƙasar na rabawa jama’ar ƙasar Naira billiyan 50. A cewar rubutu da aka buga a ranar 26 ga watan Oktoba 2021, kawai ƴan ƙasar da suka sauke suka kuma yi rigista da jakar sabon kuɗi ta eNaira a yanar gizo ne zasu samu kyautar kuɗin. Sabon kuɗi na yanar gizo na eNaira, kuɗi ne na dijital da babban bankin Najeriya CBN ya ƙaddamar ranar 25 ga watan Oktoba. Rubutun ya ce babban bankin na ƙoƙarin ganin cewa eNaira ta samu matuƙar karɓuwa. Rubutun ya ƙunshi hoton shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnan babban bankin Godwin Emefiele suna riƙe ƙaton hoto ɗauke da alamar eNaira . Shin da gaske ne za’ayi rabon Naira biliyan 50? Alamomin dafara ta yau da kullum a yanar gizo Amfanin da akayi da rubutun da ya gaza ƙa’idojin rubutu ya fara nuna cewa rubutun ba daga tushe ingantacce ya fito ba, musamman manya hukumomi. Rubutun ya kuma haɗe da wani shafi , da ba shafin babban bankin ba ne ko na eNaira. Adireshin yanar gizo na hukumomin gwamnati na ƙarewa da . gov.ng. A shafin an buƙaci masu nema da su rarraba link ɗin rubutun a WhatsApp don samun eNaira ta 50,000. Wannan misali ne na yadda ƴan damfara ke yi a Facebook don samun yawaitar masu zuwa ga rubutun su. A lokuta da dama wannan na daga cikin alamomin da ke tabbatar da ƙaryar talla. Za ku iya karanta hanyoyin da muka zayyano akan yadda zaku gano ƴan damfara a Facebook a nan ‘Ƴan damfara sun ƙara kunno kai.’ cewar CBN Bankin sun ƙaryata wata alaƙa da ƙyautar. Wannan ba gaskiya ba ne, kuma ma ba zai zama gaskiya ba. CBN bata taɓa kuma ba zata taɓa raba kuɗi ga kowa ba, Osita Nwanisobi, daraktan sadarwa na CBN, ya shaidawa Africa Check. Zamu iya samar da bashi ga jama’a, kuma zasu iya neman bashin ta bankunan da ke bada bashin akan kuɗin ruwa madaidaici. Ƴan damfara sun ƙara kunno kai, cewar Isa Abdulmumin shugaban sashen watsa labarai na babban bankin. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url