?:reviewBody
|
-
Wani rubutu da aka raba a Facebook a Najeriya ranar 6 ga watan Yulin 2022 na iƙirarin cewa babban jami’in ɗan sanda da aka dakatar Abba Kyari ya tsere zuwa ƙasar Australia bayan ƴan bindigar daji sun kai hari gidan yarin da ake tsare da shi. Rubutun na Facebook na cewa : ‘Sa’oi bayan kai hari gidan yari na Kuje, an ga Abba Kyari a ƙasar Australia.’ Rubutun na tare da wasu hotuna guda biyu, na farkon wanda ya kasance hoton allon waya ne wato sikirinshot na wani bidiyo, da ke nuna wani mutum na shiga mota, ɗaya hoton kuma na Kyari ne cikin kayan aiki. A ranar 5 ga watan Yuli , aka kai hari matsakaicin gidan gyaran hali da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja. In da firsunoni da dama suka tsere bayan maharan sun dauki sa’oi da dama a wajen. Kungiyar ƴan ta’adda ta Islamic State West Africa Province (ISWAP) ta ɗauki alhakin kai harin . Hukumar gyaran hali ta Najeriya ta fitar da sunaye da hotunan firsinoni 69 da suka tsere. Shin Abba Kyari yana cikin su, da gaske ya tsere zuwa ƙasar Australia? Mun bincika ‘Kyari bai tsere ba’ Mutumin da ke cikin hoton farko Abba Kyari ne amma hoton ba sabo ba ne. A watan Fabrairu hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta saki wannan hoton. Ta yi amfani da hoton a matsayin hujja akan Abba Kyari bayan ya amince da sakin wata hodar iblis da aka ƙwace daga wasu da ake zaton masu safarar kwayoyi ne. A ranar 6 ga watan Yuli hukumar gyaran hali ta Najeriya tace Abba Kyari da wasu ‘fursinoni na musamman’ ko jiga jigai da ake tsare da su a Kuje basu tsere ba. Umar Abubakar babban sufiritandan na gyaran hali, ya ce : A halin yanzu suna nan a tsare cikin koshin lafiya. Zambar da ake yi don samun yawaitar masu shiga shafi Rubutun na umartar masu amfani da kafar da su latse wajen da aka tanada a latsa don kallon bidiyon Abba Kyari a ƙasar Australia. Amma wajen da aka latsa ɗin na kai mutum wani shafi mara tsaro da ke ɗauke da rubutu mai taken : Gwamnatin Najeriya na yaɗa labaran ƙarya: Bamu saka IPOB a matsayin ƙungiyar ta’addanci ba, IPOB na daga cikin ƙungiyoyi masu bin doka a Britaniya- Biritaniya tayi Allawadai da Najeriya. Rubutun na yaudarar mutane, saboda a wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa, gwamnatin Biritaniya ta bayyana ƙungiyar ƴan asalin yankin Biafra a matsayin ƙungiyar ƴan ta’adda. Rubutun bashi da alaƙa da fursinonin da suka tsere daga gidan kurkukun Kuje ko Abba Kyari.
(id)
|