PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-03-18 (xsd:date)
?:headline
  • Jirgin saman yaƙi mai saukar ungulu mallakin rundunar sojojin Najeriya ya kai hari hukumar tsaro ta Eastern Security Network da ke jihar Imo? Hoton an yi shekaru uku da ɗaukar sa a Abuja (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Da ɗumi ɗumi; Rundunar sojoji na kai hari ga ƙungiyar tsaro ta Eastern Security Network da jiragen yaƙi masu saukar ungulu a jihar Imo, wannan na ƙunshe cikin kanun labaran wasu rahotanni guda biyu da aka wallafa a wani shafin yanar gizo na Najeriya ranar 17 ga watan Fabrairu 2021. Rubutun na tare da hoton jirage masu saukar ungulu guda biyu na shawagi a saman bishiyu, da mutum na riƙe da igiya daga ɗaya daga cikin jiragen. Shugaban mai fafutukar yankin Biafra Nnamdi Kalu ne ya ƙirƙiri Ƙungiyar tsaro ta Eastern Security Network a watan Disembar 2020. Kalu ya ce mayaƙan ƙungiyar tsaron ne zasu kare gabashin Najeriya daga ƴan ta’adda da ƴan bindiga daga arewa. A shekarar 1967 yankin Biafra , wanda yanki ne daga kudu maso gabashin Najeriya ya fitar da kansa daga Najeriya. Gwamnatin Najeriya tayi watsi da al’amarin, inda hakan ya jawo yaƙin basasa . An kawo ƙarshen yaƙin a watan Junairun 1970 ba tare da Biafra ta samu nasarar kafa ƙasa mai zaman kanta ba. Kalu da Ipob sun cigaba da jajircewa, tare da sabunta fafutukar neman ƴancin yankin na Biafra. A kwanan nan, sojojin Najeriya da mayaƙan ESN sun sha artabu da juna a jihar Imo wadda ke kudu masu gabashin ƙasar. Ƙarairayi da labarai marasa tushe akan rikicin tuni suka mamaye kafafe n sada zumunta . Shin wannan hoto dai dai ne? shin ya nuna jirgin yaƙi mai tashin ungulu mallakin rundunar sojojin Najeriya na kaiwa mayaƙan ESN hari a jihar Imo, a watan Fabrairu 2021? Mun bincika? Zanga-zanga da shiyar sojojin musamman sukayi a Abuja, a 2018 Kafar tantance hoto ta Google reverse image search ta nuna cewa hoton yayi shekaru kusan uku. Ɗaya ne daga cikin hotunan zanga-zangar sojoji a Gwagwalada , wata shiya da ke babban birnin tarayya Abuja, jaridar Vanguard ta buga hoton a ranar 18 ga watan Afrilu 2018. Abuja na tsakiyar Najeriya. Rubutun da jaridar tayi na ɗauke da taken: Hotuna: Shiya ta musamman ta rundunar sojojin Najeriya yayin wata zanga-zanga. Taken hoton na cewa : Ƴaƴan shiya ta musamman ta rundunar sojojin Najeriya na dirowa daga jirgi mai saukar ungulu yayin taron sojojin ƙasa na Afrika (ALFS) da akayi a barikin Janar AO Azazi da ke Gwagwalada a ranar 17 ga watan Afrilu 2018. Taron sojojin ƙasa na (ALFS) taron ƙarawa juna sani ne na mako guda da aka gudanar a Najeriya. Taron ya haɗa sojojin ƙasa daga ko’ina a Afrika don tattauna da samar da hanyoyin da za’a haɗa kai don magance matsalar tsaro tsakanin ƙasashen. Hoton na taron AFP ne. Hoton bai nuna jirgin rundunar sojojin Najeriya na kaiwa ESN hari a jihar Imo a watan Fabrairu 2021 ba. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url