PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-12-10 (xsd:date)
?:headline
  • Kar kuyi maganin matsalar tairod da hadin itatuwa (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani saƙo da ke yawo a Facebook a Najeriya na cewa maganin gida na taimakawa wajen maganin tairod, maganin warin baki, kwayoyin cuta a huhu da kumburin wuya (maƙoƙo). Saƙon ya bada shawarar haɗa magunguna daga Aidan, shuɗin ƙaro, ƴaƴan lara da zuma, a sha rabin kofi kullum kafin a ci abinci. Tetrapleura tetraptera wanda Yarabawa ke kira da aidan, ɗan itace ne da ya samo asali daga yankin Afrika mafi zafi, an kuma yadda itacen na da amfani da kuma magani a jiki. Lara na nufin itacen man kasto a harshen Yarabanci, wanda ake noma shi don haɗa magunguna a kuma sayar. Shin wannan haɗin magunguna na magance matsalar tairod? Mun bincika. Maƙoƙo shine kumburin tairod Sashen jiki da akafi sani da tairod gilan ana samun sa a gaban wuya. Shine kuma ke samar da sinadarin halitta na homons wanda ke da matuƙar muhimmanci wajen yin wasu ayyuka a jiki. Shi kuwa maƙoƙo kumburin tairod ne wanda ba na al’ada ba, wanda baya ciwo. Ba lalle ne ya shafi aikin tairod ba, ko ya jawo yawa ko raguwar sinadarin tairod ba. Abubuwan da ke jawo maƙoƙo sun haɗa da kumburin tairod, ko tairod ɗin ya ringa aikin da ya gaza ko ya wuce ƙa’ida, sauyin sinadarin halitta wato homos, sankarar tairod, da kuma rashin sinadarin ayodin a abinci. Ana da masu fama da maƙoƙo kaɗan a ƙasashen da ake saka sinadarin ayodin a gishirin da ake amfani da shi. Ƙaramin maƙoƙo ba ya ciwo, amma idan yayi tsanani ya na iya jawo tari, wahalar haɗiyar abu da wahala wajen yin numfashi. Ana maganin sa da magunguna ko ayi aiki Aihanuwa Eregie, Farfesa a fanin magungunan da cututtukan da suka shafi sinadaran jiki da tsokokin ƴaƴan halitta na jami’ar Benin a kudu masu yammacin Najeriya, ta shaidawa Africa Check bata yadda ayi maganin tairod da haɗin itatuwa ba. Maƙoƙo kawai kumburin sashen jiki da aka fi sani da tairod ne, kuma ana maganinsa bayan anyi la’akari da yanayin sa. Ta hanyar bada magani ko yin aiki, ta ƙara da cewa. Idan maƙoƙo yaƙi jin magani, sannan yana jawo wahala wajen numfashi ko haɗiya, hukumar kiwon lafiya ta Biritaniya tace sai ayi aiki don cire shi ko wani sashe na tairod ɗin. (so)
?:reviewRating
rdf:type
?:url