PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-07-27 (xsd:date)
?:headline
  • Hukumar shige da fice ta Najeriya bata ɗaukar ma’aikata a Facebook- Zamba ce (sw)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani saƙo da ke yawo a Facebook na iƙirarin cewa hukumar shige da fice ta Najeriya ta gabatar da shirin ɗaukar ma’aikata na 2022. Shirin ɗaukar ma’aikata na hukumar shige da fice ta Najeriya 2022- Ana son sanar da ku cewa an fara ɗaukar ma’aikata a hukumar shige da fice ta Najeriya. Ku duba wajen da ake shigar da bayannan waɗanda ke neman aikin a yanar gizo, saƙon ya ce . Sannan saƙon ya ƙara da bada wajen da za’a latsa a shiga wani shafi da ake so mutane su shiga su cike gurbin neman aikin. Wani saƙon kuma yana sanar da matasa da su tuntuɓi Adetunji Adebayo akan layin waya 08062549981 don samun ɗaya daga cikin ayyuka don matasa guda 10 da ake da su. Amma waɗannna ayyuka na gaske ne? Mun bincika. ‘Wani babban salon damfara daga wasu ƴan damfarar’ Wajen da aka tanada don a latsa a cikin saƙon na zuwa wani shafi mai sunan da ba’a saba gani ba, wato Celebidentity. Shafin na nuna an ƙirƙire shi a ranar 30 ga watan Yuni 2022, ya kuma ce ga masu neman aikin shige da fice za’a rufe ƙarbar takardun neman aikin ranar 31 ga watan Yuli. An tallata wasu guraban aiki ma a shafin. A ranar 1 ga watan Yuli, hukumar shige da fice ta Najeriya ta wallafa wata sanarwa a shafinta na Facebook tana gargaɗin cewa guraban aikin da ake bayarwa na ƙarya ne ba daga hukumar suka samo asali ba. Sanarwar na da taken: A KIYAYI MASU IƘIRARIN SAMAR DA AIKI NA DAMFARA: BAMA ƊAUKAR MA’AIKATA. An jawo hankalin shugaban hukumar shige da fice Isah Jere Idris akan wata sanarwa da ke yawo a kafafan sada zumunta da ke bayyana cewa hukumar na ɗauka/cike gurbin ma’aikata, sanarwa ta ce . Yana da muhimmanci na bayyana cewa rubutun ba komai ba ne, fa ce wata hanya babba da mazambata suka shirya don yaudara da damfarar jama’a gumin su akan ayyukan da kwata-kwata ma babu su. Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Okpu Amos ne ya sanyawa sanarwar hannu. Ya kuma ƙara da cewa lokacin da hukumar zata tallata guraban aiki, tana amfani da kafafen sada zumunta fitattu kuma waɗanda aka saba amfani da su da suka haɗa da shafukan hukumar. Africa Check ta ƙaryata damfarar yanar gizo da dama da ke tallata aikin yi, basussuka da kyaututtuka. Ku karanta yadda zaku gane hanyoyin da zaku gano su. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url