?:reviewBody
|
-
Wani bidiyo da aka saka a Facebook Najeriya a watan Afrilu 2022 na nuna gungun maza, waɗanda ke ɗauke da bindigogi akan titi a karkara. Da farko an nuno su suna ta yawo a wajen, suna maganganu, sai kuma aka ji waƙa ta fara tashi har aka ga suna rawa. WANNAN ƘASA TA TASHI DAGA AIKI, taken da ke tare da bidiyon waɗanda aka rubuta su da manyan harufa ke cewa . ƳAN FASHIN DAJI SUN TOSHE TITIN ABUJA ZUWA KADUNA SUNA JIRAN ABABEN HAWAN DA ZASU YI GARKUWA DA SU. An kalli bidiyon sama da sau miliyan 1.4, mutane 6,700 sun yi tsokaci akan bidiyon, yayin da aka kuma rarraba bidiyon sau dubu 25,000. Titin Abuja zuwa Kaduna, titi ne da ke tsakiyar ƙasar kuma ya ke haɗa babban birnin tarayyar Najeriya da garin Kaduna , wanda gari ne mai muhimmanci a arewacin Najeriya. Titin ya shahara da hare-hare wanda ya haɗa da garkuwa da mutane. An saka bidiyon ne bayan harin da ƴan bindiga suka kaiwa jirgin ƙasa a hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja ranar 28 ga watan Maris. Inda aƙalla mutane 8 suka rasa rayukansu . Yayin da mutane 168 ake zargin an yi garkuwa da su ko sun ɓace. Amma shin bidiyon mai tada hankali, ya nuno ƴan fashin daji akan titin Abuja zuwa Kaduna a watan Afrilu suna jiran ƙarin mutanen da zasuyi garkuwa dasu? ‘Bidiyon dai bashi da kwanan wata’ an fitar da shi a watan Janairun 2022 Ciyayi masu haske, harshen da mazan ke magana da shi da waƙar da aka ji a cikin bidiyon duk na nuna alamun an ɗauki bidiyon a arewacin Najeriya. Sai dai titin layi ɗaya ne wanda babu wata alama akan sa. Yayin da titin Abuja zuwa Kaduna tituna ne guda biyu , kowanne titi kuma an masa alama a bayyane. Mun kuma gano cewa bidiyon ya shafe aƙalla watanni huɗu a yanar gizo- idan ma bai fi haka ba. Tashar YouTube ta Sahara ta ɗora bidiyon a watan Janairu da taken ‘bidiyo mara kwanan wata na wasu gungun ƴan fashin daji da suka haɗa da sojoji yara suna rawa. Bidiyon ya fito a yanar gizo tun kafin a kai mummunan harin da aka kaiwa jirgin ƙasa a watan Maris.
(so)
|