PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-07-19 (xsd:date)
?:headline
  • Ɗaukar ma’aikata a Najeriya? Tallan na bogi ne (sw)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani saƙo da ke ta yawo a WhatsApp da Facebook a watan Yulin shekarar 2021 na iƙirarin cewa Hukumar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta Najeriya na ɗaukar ma’aikata aiki a ma’aikatu da sassa da kuma hukumomi da dama. SANARWAR ƊAUKAN MA’AIKATA A HUKUMAR MA’AIKATAN GWAMNATIN TARAYYA TA NAJERIYA, abun da saƙon mai cike da kuskuren rubutu ke cewa . Ya kuma haɗo da shafin da jama’a zasu iya neman aikin. Amma waɗannan guraben aiki gaskiya ne? Mun bincika. Babu tallan a shafin hukumar na yanar gizo Mun bincika shafin hukumar ko zamu ga tallan aikin, amma bamu gani ba. A shekarar 2019 FCSC ta gargaɗi jama’a akan tallan ɗaukar aiki dake yawo a yanar gizo na ƙarya. Don gujewa shiga shakku, duk aikin ɗaukar ma’aikata da hukumar zata yi, zata buga a shafinta na yanar gizo , jaridu da gidajen talabijin da rediyo, hukumar ta ce. Hukumar ta ƙara da cewa bata tallata ɗaukar aiki a kafafen sada zumunta. Shafukan yanar gizo na bogi Akwai wasu alamu da ke nuna cewa wannan ɗaukar aiki da ake tsammanin ana yi ƙarya ne. Adireshin shafin- wato URL- an taƙaitashi ta amfani da Bitly . Shi kansa shafin an tsara shi ba tare da kwarewa ba kuma yana kama da na bogi , suna kuma tambayar masu neman aikin da su bada bayanan su na sirri. Bugu da ƙari kuma lokacin da Africa Check ta ziyarci shafin bayan wasu kwanaki sai shafin ya mai da su wani shafin na daban, mai taken MTN Science & Technology Scholarship Scheme Form. Da farko shafin yayi iƙirarin cewa sama da yan Najeriya 140,000 ne suka nemi aikin na FCSC, kuma an duba sama da 16,000- wanda hakan ya basu matsakaicin matsayi na 4.8 daga cikin 5. Duka shafukan na FCSC da MTN sunyi amfani da yankin .xyz, maimakon yankin da gwamnatin Najeriya ke amfani da shi na gov.ng . Wannan shine (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url