PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-09-30 (xsd:date)
?:headline
  • Allurar rigakafi ba zata sa ku zama ‘marasa iri’ ba (sw)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Matuƙar zasu iya mai da ɗan itace mara iri, zasu iya mayar da KU marasa iri ku ma, wani hoto da ke yawo a Facebook ke cewa . Hoton ya nuno kankana babu ƴan ƴan ƙwallayanta, a saman hoton kuma hannu ne a cikin abun rufe hannu na asibiti da sirinjin allura a hannun. Daga gani dai ana ƙokarin hana yin allurar rigakafin Covid-19 ne. An turowa Africa Check hoton a matsayin tsokaci, biyo bayan saƙon shirin wayar da kai na #KuSanGaskiyaKuKarɓiAllurarRigakafi ta shafin Twita. Tsokacin ya haɗa da wannan bayanin : Ƴaƴan itatuwan da aka sauya ƙwayoyin halittar su basu da ƴaƴan ƙwallaye. Da zarar kun ƙarɓi allurar rigakafin ku ma zaku zama an sauya ƙwayoyin halittar ku. Mallaka da haƙƙin mallakar ƴancin masu yin allurar rigakafi zai ɓace ɓakatatan. Hanyar rage al’umma itace zaku zama marasa iri. Wannan da’awar ƙaryar an tantance ta sau da dama. Alluran rigakafi, waɗanda suka haɗa da alluran rigakafi na mRNA da akayi don kiyaye kamuwa da Covid-19, ba zasu sauya ƙwayoyin halittar mutum ba. Ba za kuma a iya ƙwatanta mutum da ɗan itace ba. Ku ba ƴaƴan itacen da ba ku da ƙwallayen iri ba ne Ba sauya ƙwayoyin halitta ne ya ke samar da ƴaƴan itacen da basu da ƙwallaye ba. Kamar yadda kwalejin aikin noma da albarkatun ƙasa ta jami’ar jihar Michigan ta rubuta a shekarar 2019 : A yanzu babu wasu itatuwa marasa iri da aka sauya ƙwayoyin halittar su(GMOs). Itatuwa na samar da ƙwallon iri a halicce, haka nan ana noman marasa iri kamar yadda mutane ke noma kowanne amfanin gona. Rashin ƙwallon iri halitta ce, jihar Michigan ta bayyana cewa, Ɗabi’un gado da ake ɗaukar su ta hanyar folin kuma ƙwayoyin halitta ke riƙe su har sai mahaɗin su ya samu hanyar daidaiton iyayensu, shi ya ke samar da itatuwa masu iri. Amma maimakon kai tsaye a sauya ƙwayar halittar itatuwa ta DNA, mutane suna kawai zaɓar su shuka itatuwan da ke fitowa ba tare da iri ba. Za kuma a iya samar da itatuwa marasa iri ta wasu hanyoyin daban. Wasu itatuwa na samar da ƴaƴan itatuwa marasa ƙwallo idan har an gurɓata furensu- amma mutane zasu iya kiyaye afkuwar hakan. A bayanan Encyclopedia Britannica ance ana iya samar da itatuwan marasa ƙwallo ta hanyar bijirarwa da wasu itatuwa wasu sinadarai, ana hakan kuma tun shekarar 1934. Mutane da dama zasu iya zama marasa haihuwa - wanda ke nufin ba zasu iya ɗaukar juna biyu ba. Amma rashin haihuwa ga bil adama ko kusa ba dalilai ɗaya ba ne da rashinta ga itatuwa. Babu wata hujja da ta tabbatar cewa allurar rigakafin Covid-19 - ko wasu alluran rigakafin da aka saba yi- zasu iya jawo rashin haihuwa Alluran rigakafin Covid-19 ba sa sauya ƙwayoyin halittar ɗan adam na DNA Almara ce ace allurar rigakafin Covid-19 na sauya ƙwayar halittar ɗan adam ta DNA. Wannan da’awar wadda ta fi magana akan alluran rigakafi na mRNA , an sha tantance cewa karya ce, har ma Africa Check sun taɓa ƙaryata ta. Ɗan aiken RNA , ko mRNA abu ne da ke ɗaukar bayanan ƙwayar halitta. Amma ba ɗaya suke da DNA ba, wanda ke adana ƙwayoyin halittar jini. Sai dai mRNA na bawa jiki umarnin samar da wasu firotin. Alluran rigakafin Covid-19 na mRNA na bawa jiki umarnin gina sifayik firotin, wani tsari na musamman ga ainihin ƙwayar cutar. Wannan shi zai bawa jiki damar gina sifayik firotin, wanda zai samar da matakan yaƙar ƙwayar cutar Masana kimiyya a ɗakin bincike na Meedan Digital Health Lab sun ce : Kafin a sauya ƙwayar halitta ta DNA, dole ne ya zamana an gabatar da ƙwayar halittar jini daga wani abu mai rai an sa a cikin tsakiyar tantanin jikin mutum mai ɗauke da DNA ɗin su. Shi mRNA da ke jikin alluran rigakafin Covid-19 baya shiga tsakiyar tantanin ya kuma karye cikin awanni 72 ba. (sw)
?:reviewRating
rdf:type
?:url