PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-04-14 (xsd:date)
?:headline
  • Gargaɗi akan ƴan damfara! KPMG basuyi tallan shirin horar da waɗanda suka kammala digiri a Facebook Najeriya (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • KU CIKE NEMAN IZINI: Shirin waɗanda suka kammala digiri na KPMG na shekarar 2022, abun da wani saƙo da ke yawo a Facebook da WhatsApp Najeriya ya fara da shi. KPMG cibiya ce ta duniya da ke ƙunshe da kamfanunnukan da suke binciken kuɗi, haraji da bada shawara. Abun da ake buƙata: Digiri na farko ko babbar difiloma. Ba’a buƙatar shekarun ƙwarewar aiki. Wa’adi: 15 ga watan Afrilu 2022. saƙon ya ce . Saƙon ya ƙare da bawa jama’a ƙarfin gwiwar sake rarraba damar a wasu guruf-guruf na shafukan sada zumunta kafin wa’adin ya cika. Saƙon na ɗauke da alamar da za’a latsa wadda zata kai mutum shafin yanar gizon da za’a cike gurbin neman horon. Shin tallan na gaskiya ne? KPMG sun fitar da gargadi KPMG Najeriya a ranar 11 ga watan Afrilu sun fitar da gargaɗi a Facebook da Twitter cewar tallan na bogi ne. An jawo hankalin mu akan masu ƙarya da sunan KPMG, suna yaɗa tallan ƙarya a kafafen sada zumunta da yanar gizo, gargaɗin ya ce . A kiyaye cewa mu, muna saka ayyuka, hanyar binciken masu zartarwa ( ga abokan hulɗar mu) a shafin mu na yanar gizo da kuma shafukan mu na sada zumunta. Don haka ba zamu ɗauki alhakin duk abun da ya biyo bayan saɓanin hakan ba. Africa Check ta tantance da ƙaryata damfarar yanar gizo da dama akan bada gurbin aiki, tallafi, bashi da kuma kyaututtuka. Ku karanta nan don gane yadda zaku gane masu damfara. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url