?:reviewBody
|
-
Wani bidiyo a Facebook wanda ya samu masu kallo sama da sau miliyan 4.5, ya bada yadda za’ayi magani ta hanyoyin asali, kowanne bayani an fara shi da jimlar Shin kun sa ni? Ɗaya daga ciki na cewa idan kun sha ruwa kafin ku ci komai da zarar kun tashi daga bacci zai hana ku kamuwa da kuma yi muku maganin cutar asma da matsalolin zuciya. Africa Check ta taɓa tantance wasu da’awowin da ke cikin bidiyon: cewar ganyen mullein na maganin kwalta da majina daga huhu da kuma cewar saka tafarnuwa a cikin kunne na maganin ciwon kunne da ciwon kai. Mun kuma ƙaryata da’awar da ke cewa shan ruwa a lokacin da ya dace na taimakawa wajen kiwon lafiya. Amma shan ruwa da an tashi da safe na magani da hana kamuwa da ciwon asma da ciwon zuciya? Mun bincika. Shan ruwa yana magani da kiyaye kamuwa da asma? Asma cuta ce da ke cikin huhu, wadda ke sa wahala wajen yin numfashi. Cutar na da alamomi kamar huci, ɗaukewar numfashi, ɗaurewar ƙirji da tari. Farfesa Keertan Dheda, darakta a cibiyar cutar huhu da garkuwa daga cututtaka , kuma shugaban sashen kula da cutukan huhu na jami’ar Cape Town , ya ce, babu gaskiya a wannan batu. Akwai matakan da za’a iya bi don hana tashin cutar asma, amma cutar karan kanta ba’a hana kamuwa da ita, a cewar Mayo Clinic . Babu wani bayani na yadda yake kasancewa wasu mutanen na da cutar asma amma wasu basu da ita, amma ta iya yiwuwa saboda abubuwan da suka danganci muhalli da kuma gado. Ana amfani da abun shaƙa na inhaler wajen maganin asma, inhaler na sa a shaƙi maganin da zai hana tashi ko yayi maganin ciwon idan ya tashi, ko kuma a sha magani. Kuma ciwon zuciya fa Ciwon zuciya ko cututtakan zuciya da jijiyoyin jini , na nufin cututtakan da ke kama zuciya da hanyoyin jini kamar cutar zuciya da jijiyoyin jini da kuma cutar jijiya . A shekarar 2021 wani bincike da masana daga cibiyar zuciya, huhu da jini ta ƙasa a Amurka suka yi wanda aka buga a mujallar European Heart Journal sun binciko cewa kasancewar jiki da isasshen ruwa na rage hatsarin gazawar zuciya, ya kuma rage tsayawar zuciya. Amma bamu samu hujjar da ta tabbatar mana da cewa shan ruwa da zarar an tashi daga bacci kafin a ci komai na magani ko hana ciwon zuciya. Wannan ba magani ne mai hujja ba, Dr Nqoba Tsabedze malami kuma shugaban shiyar kula da zuciya na jami’ar Witwatersrand , ya shaida mana. Sai dai za’a iya rage hatsarin kamuwa da cutukan zuciya ta hanyar motsa jiki akai- akai da bacci, gujewa cin abinci mai kitse da abincin gwangwani, a yawaita cin kayan lambu da ƴaƴan itatuwa, rage cin gishiri, gujewa shan sigari da kula da rage wahalar da jiki. Duba da irin yanayin ciwon zuciyar da ake da shi, magani ya haɗa da ingantaccen abinci, motsa jiki, chanji ga yanayin rayuwa, magunguna da kuma yin aiki ko tiyata.
(so)
|