?:reviewBody
|
-
A TAƘAICE: Mun ta cin karo da labaran ƙarya masu tarin yawa da ke ta yawo a shafukan sada zumunta a Najeriya tun bayan mai sa ran yin shugabancin Najeriya Bola Tinuba shiga takara a ƙarƙashin jam’iyya mai mulki a watan Janairun 2022. Kamar sauran da’awowi da dama, a kwanan nan ma, jita-jitar da ake yaɗawa cewa ya janye daga takara, ƙarya ce. Bola Ahmed Tinubu zai janye daga takarar shugaban ƙasa saboda dalilan da suka danganci lafiya, wani saƙo da aka yaɗa a wani guruf a Facebook da ke ɗauke da mutane sama da 46,000 ya fara da cewa. Saƙon na iƙirarin cewa Bola Tinubu zai fita daga cikin ƴan takarar zaɓen Najeriya na shekarar 2023 bisa shawarar likitan sa, wanda ya ce ya ajiye buƙatar sa na son yin shugabancin ƙasa saboda lafiyarsa. Rubutun na cewa : Likitocin da ke kula da lafiyar ɗan takarar shugaban ƙasar da bashi da cikakkiyar lafiya daga jam’iyyar APC Mr Yekini Amoda (da aka fi sani da Bola Ahmed Tinubu), likitocin sun bashi shawarar janye takarar son zama shugaban ƙasa daga yanzu. Rubutun ya ce ya samo labaran ne daga kamfanin dillancin labarai na Reuters . Tinubu ɗan takarar shugaban ƙasa ne daga jam’iyya mai mulkin Najeriya All Progressives Congress (APC), ɗaya daga cikin manyan ƴan takarar babban zaɓen ƙasar na 2023. Ya taɓa yin gwamnan jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya. Tun lokacin da Tinubu ya bayyana ƙudurinsa na yin takarar shugabancin ƙasar a watan Janairun 2022, ake ta hasashen ainihin shi waye da kuma yanayin lafiyarsa . A ranar 29 ga watan Satumba, kwana guda bayan fara yaƙin neman zaɓe a ƙasar, ƴan takarar shugabancin ƙasar sun rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya , wadda sukayi a birnin tarayyar Najeriya, Abuja. Amma rashin zuwan Tinubu wajen sanya hannun ya assasa jita-jitar da ake akan lafiyarsa. Mun samu wasu rubuce-rubucen akan janyewar Tinubu daga takarar a Facebook a nan , nan da nan . Amma waɗannan jita-jita gaskiya ne? Mun bincika. ‘Da ƙarfinsa da lafiyarsa, kuma a shirye ya ke don hidimtawa jama’a’ Binciken da mukayi a shafin Reuters na yanar gizo ba mu ga inda aka kawo rahoton janyewar Tinubu ba daga takara. A ranar 2 ga watan Oktoba, Bola Tinubu ya wallafa a sahihin shafin sa na Tiwita , yana ƙaryata da’awar cewa ya janye takara. Ya rubuta kamar haka: Da dama sun ce na mutu; wasu sunyi iƙirarin cewa na janye daga yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasa. Sai dai ..... Ba haka ba ne. Ya ce yana nan da ƙarfinsa da lafiyarsa, a kuma SHIRYE ya ke ya hidimtawa ƴan Najeriya daga ranar da zai hau. Ɗan shekaru 70 ɗin, ya saka hotonsa da ya ɗauka yana kan keken motsa jiki. A ranar 10 ga watan Oktoba a Abuja, Tinubu ya ƙaddamar da ɓangaren mata na yaƙin neman zaɓensa . Babu wata alama da ta nuna cewa yaƙin neman zaɓen nasa na ja da baya.
(id)
|