?:reviewBody
|
-
A TAƘAICE: A wasu saƙonni da aka wallafa a kafafen sada zumunta a Najeriya, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya nuna kamar ya tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar APC- Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar sa na shugaban ƙasa. Maganganun ƙirƙirar su akayi kuma tsayar da shi da ake cewa yayi, ƙarya ce. Wani hoton allon waya wato sikirinshot da ke yawo a Facebook Najeriya na ɗauke da wasu maganganu da suka bayyana cewa daga bakin tsohon wanda yayi shugabancin ƙasar nan har sau biyu Olusegun Obasanjo suka fito, suna cewa ya tsayar da Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa mai jiran gado. Tinubu tsohon gwamnan jihar Legas ne, wadda ke kudu maso yammacin Najeriya, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyya mai mulki All Progressive Congress . Rubutun jikin hoton allon wayar wanda ke haɗe da hoton Obasanjo da Tinubu, ya na cewa; Ni ba ɗan siyasa ba ne, ni soja ne da aka karrama kuma mai muƙamin janar na sojojin ƙasa. Idan kuna neman cikakken ɗan siyasa, na ajin farko ku je Bourdillon da Legas, a nan zaku same shi. Tinubu na zaune a titin Bourdillon da ke unguwar Ikoyi a Legas, wanda rukunin gidaje ne na masu faɗa aji . Bayan a bayyane sun yi iƙirarin cewa wai ya kusa hallaka gwamnatin Tinubu da jiharsa, an kuma ruwaito Obasanjon na cewa wai Tinubu ya tsallake ne saboda yana da wani ƙarfi na daban. Mu na fatan zai samu damar nuna wannan ƙarfi a Najeriya. Obasanjo yayi shugaban Najeriya a lokacin mulkin soja tsakanin shekarun 1976 zuwa 1979, sannan yayi shugaban ƙasa a matsayin farar hula a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007 a ƙarƙashin jam’iyyar People’s Democratic Party. Hoton allon wayar da aka buga a ranar 7 ga watan Oktoba 2022, an sake wallafa shi a nan da nan . Amma Obasanjo ya bayyana Tinubu a matsayin cikakken ɗan siyasa’’ kuma mai wani ƙarfin iko Obasanjo: Wannan ƙarya ce kuma bogi Obasanjo ya musanta cewa ya tsayar da Tinubu a wata sanarwa da mataimakinsa akan yaɗa labarai Kehinde Akinyemi ya fitar. A wata sanarwa da Africa Check ta samu, Obasanjo ya ce: Rundunar Soja ce kawai take horar da jami’anta su zama masu iya juya jama’a da abubuwa. Don haka, ba zan ci mutuncin aikina na siyasa ba wanda baya buƙatar wani horo na musamman. Wannan ƙarya ce kuma bogi. Manyan wuraren yaɗa labarai da dama sun wallafa wannan sanarwar suna jayayyar tsayarwar da aka ce Obasanjo ya yiwa Tinubu. Ƙarya ce.
(id)
|