?:reviewBody
|
-
Kun san cewa ganyen muliyan na taimakawa wajen wanke huhu daga kwalta, yawu mai yauƙi da majina? wani rubutu a akan wani hoto a wani saƙon Facebook ke tambaya. Yana buɗe hanyoyin iska, yaƙar cutar asma da matsalolin huhu. Hoton na da taken TSAFTACE HUHU. Muliyan , wani ganye ne da ya fito daga gidan nau’in ganyayyaki masu suna verbascum thapsus, ya samo asali daga Afrika ta arewa, Asia da Turai. Wannan iƙirari akan cewa yana tsaftace huhu gaskiya ne? Mun bincika. Babu hujjar da ta tabbatar da da’awar Dr Richard Raine , likitan huhu a asibitin kula da masu lalurar numfashi a asibitin Groote Schuur da jami’ar Cape Town kuma ɗan ƙungiyar masana lafiyar ƙirji ta Afrika ta Kudu , ya ƙaryata da’awar. Ya ce babu wata hujja a yanzu a kimiyance da ta tabbatar da hakan. Hanyar da tafi wajen zama cikin lafiyar huhu shi ne a guji zama wajen da za’a iya shaƙar hayaƙin taba da sauran hayaƙi, shaƙe-shaƙe da kuma muhalli mai gurɓatacciyar iska. Asma ‘na da tsanani kuma zata iya zama barazana ga rayuwa’ A cewar asibitin Mayo, wata cibiyar ɗaukar karatun magunguna da ke Amurka, asma cuta ce da ke sa hanyoyin numfashi su ƙanƙance su kumbura , su kuma fitar da majina mai yawa. Wannan na sa wahala wajen yin numfashi, ya sa tari, da fitar sauti yayin fitar da numfashi da kuma ɗaukewar numfashin. Matsalolin da suka danganci muhalli ko halitta ke jawo cutar. Raine ya ce, asma cuta ce mai tsanani kuma zata iya zama barazana ga rayuwa wadda ke da magunguna a kimiyance, da manya masana kiwon lafiyar numfashi a duk faɗin duniya suka amince dasu. Ganyen muliyan baya cikin magungunan. Magungunan da ake bayarwa na ƙara inganta rayuwa, su rage yawan zama a asibiti, su kuma kiyaye mutuwa daga cutar idan ta tsananata. Idan kuna fama da ciwon huhu kuje kuga likita, wanda zai duba ya gano matsalar ya bada maganin da ya dace.
(sw)
|