PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-03-18 (xsd:date)
?:headline
  • Haɗi mara tushe: Ɗakin gwaji na Wuhan ba mallakin GlaxoSmithKline ba ne, bai kuma mallaki Pfizer ba (sw)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Ɗakin gwaji na ƙasar Sin da ke Wuhan mallakin GlaxoSmithKline ne, abun da ke ƙunshe kenan cikin wani saƙo da ke ta yawo a kafar Facebook . Rubutun ya cigaba da cewa , kamfanin yin magunguna na GlaxoSmithKline ne ya mallaki kamfanin Pfizer , wani kamfanin yin magunguna. Kamfanin Pfizer ya fitar da rigakafin koronabairas, wacce ta samo asali daga Wuhan, China a ƙarshen shekarar 2019. Rubutun ya haɗa waɗannan kamfanunnuka da wasu manya da ake shirya makirce- makirce akan annobar Covid-19 da sunayen su, waɗanda suka haɗa da shugaban kamfanin Microsoft Bill Gates da Dr Anthony Fauci , shugaban cibiyar cututtuka masu yaɗuwa ta Amurka . Maƙarƙashiyar makirci ko arashi? abun da rubutun ya fara ƙunsa. Ya nuna cewa mutanen, kamfanunnukan da hukumomin da aka ambata na da hannu wajen annobar Covid-19. Rubutun ya nuna cewa Pfizer ne suka ƙirƙiri allurar rigakafin cutar. Shin da gaske duk waɗannan abubuwan na da alaƙa da juna? Da’awar ta yi wata bakwai kuma har an tantance cewar ƙarya ce Babu dai tabbacin sanda aka fara yaɗa da’awar, amma Africa Check ta samo irin da’awar, wadda ta gano cewa an fara yaɗa ta a watan Nuwanbar 2020. Masu tantance labarai na Reuters sun tantance ta a watan Disemba har sau biyu , haka ma Australian Associated Press sun tantance ta. Rubutun ya ta’allaƙa akan cewa annobar Covid-19 ta samo asali ne daga wani ɗakin gwaji da ke Wuhan, wadda aka alaƙanta ta da GlaxoSmithKline da Pfizer. Abun ba haka ya ke ba. Da farko dai, babu hujjar da ta tabbatar da cewa Covid-19 ta samo asali daga ɗakin gwajin ƴaƴan halitta a Wuhan. Masana sun yi watsi da wannan batu, sun dai yadda cewa ƙwayar cutar ta yaɗu ne daga jamage zuwa ga ɗan Adam ta hanyar nau’in wata dabbar. Babu wata alaƙa tsakanin cibiyar ƙwayoyin cuta da ke Wuhan da GSK. Cibiyar bata ambaci GSK a matsayin abokan huldar ta ba a shafinta na yanar gizo. Shafin dai ya ce cibiyar Chinese Academy of Sciences ne suka ƙirƙiri cibiyar kuma suka mallake ta. Haka nan GSK ba ita ta mallaki Pfizer ba. A shekarar 2018, kamfanunnukan biyu sun amince zasu haɗe rassan su da ke kula da lafiyar masu amfani da abun da su ke sarrafawa, ta yadda kashi 68% zai zama mallakin GSK. Baya ga haka kowanne daga cikin su zaman kansa ya ke, sannan haɗakar bata haɗa da ayyukan bincike da cigaba ko rigakafi, ko rassan kowanne daga ciki ba. Wannan itace kawai alaƙar da rubutun na Facebook ya bayar ba dai dai ba. Da yawa daga cikin alaƙoƙin da aka ambata basu da tushe, yayin da sauran ke yaudarar mai karatu. Ga dai duka alaƙar da rubutun ya ambata da hujjojin da Africa Check ta binciko( waɗanda sau tari suka kasance saɓanin abun da suka faɗa). Akwai mahaɗun da ba’ayi amfani da su ba Ba Dr Anthony Fauci ba ne ya ƙirƙiri cibiyar ƙwayoyin cuta ta Wuhan. Kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya yi bayani , mafi kusanci da gaskiya a wannan bayani shine cewa tsakanin 2015 da 2019 an bawa cibiyar tallafi daga wata ƙungiya, wadda US National Institute of Health ke tallafawa wadda cibiyar kula da lalurar alaji da cututtaka masu yaɗuwa da Fauci ke jagoranta ke ciki. Duka BlackRock da Vanguard na da jari a GSK ( BlackRock na da kashi 7.5% na jari), wadannan biyu ne daga cikin kamfanunka 1,528 da ke da jari a GSK . Don haka ba za’ace BlackRock ke tafiyar da GSK ba, sam ba haka ba ne . Kuma ba BlackRose ne ke sarrafa kuɗaɗen Open Society Foundations ba. Mamallakkin Open Society , George Soros ke bawa gidauniyar kudi. Babu kuma hujjar da ta nuna cewa hukumar na wa French AXA aiki. Kamfanin inshora mallakin ƙasar Faransa AXA bai ambaci Open Society Foundations ba acikin taswirar tsarin ƙungiyar ba , sannan babu hujjar cewa sun karɓi tallafi daga Open Society ko wani tallafi na daban. A shekarar 2006, AXA ta mallaki kamfanin Swiss Company Winterthur , wanda rubutun na Facebook ya ce Soros ne ya mallaka. Hukumar US Securities Exchange ta na tattara bayanan masu rijistar kamfani har 3000 a kullum a laburaren tattara bayanai, nazari da bincike (Edgar). Wannan ya nuna cewa, duk da cewa akwai alaƙa tsakanin Vanguard da BlackRock( bayanan kwanan nan na nuna BlackRock ya mallaki kashi 14.6% na jarin American Vanguard Corporation), Vanguard bata da alaƙa da Allianz SE ( wadda ke da hediƙwata a Jamus), sannan Allianz ta bayyana AXA a matsayin abokin gasarta (ba reshenta ba). BlackRock ya mallaki sama da kashi 5% na jarin Microsoft, hakan na nufin (kamar yadda rubutun na Facebook ya ambata) a matsayin babban mai hannun jari. Amma rubutu bai yi dai dai ba da ya kira Microsoft mallakin wanda ya ƙirƙire shi, Bill Gates. Gates ba shine mafi rinjaye a cikin waɗanda suka mallaki Microsoft ba tun 2014, bama yana cikin masu bada shawara a Microsoft. Gates ba ya cikin masu hannun jari a Pfizer, amma gidauniyar Bill da Malinda Gates ta bawa Pfizer tallafi a 2019 don yin bincike a kan cutar Nimoniya, a cewar bayanin harajin gidauniyar . Haka nan, Gates ba shi ne ya fi bada tallafi mafi tsoka ba ga hukumar lafiya ta duniya, amma gidauniyar Gates ce ta bada tallafi mafi tsoka ga WHO a ƙarshen shekarar 2020. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url