?:reviewBody
|
-
Wani saƙo da ke ta yawo a shafukan Facebook a Najeriya na cewa wai haɗin albasa, shuwaka da zuma zai magance cutar sikari nau’i na 1 da na 2. Saƙon ya bada umarnin a markaɗa’ albasa guda 6’, sannan a haɗa da’ ganyen shuwaka cikin tafin hannu’ ko wani itace da ake kira vernonia amygdania , sannan a saka zuma a cikin haɗin. Saƙon ya ce a sha babban cokali biyu na haɗin safe, rana da dare tsahon makwanni biyu, tabbas za’a ‘warke sarai’ daga cutar. Ciwon suga nau’i na 1 na afkuwa ne lokacin da aka ce fankiriyas na cikin mutum ya gaza samar da isasshan sinadarin insulin a jikin mutum. Sinadarin insulin shine sinadarin da jikin mutum ke amfani da shi wajen amfani da sikari ko maikon da ke shiga jiki. Ciwon suga nau’i na 2 wanda aka fi sani da rashin amsar insulin , na afkuwa ne lokacin da jiki ya ƙi karɓar insulin din da fankiriyas ke fitarwa ko ya ƙi amfani da shi yadda ya kamata. Shin wannan haɗin na gida zai magance cutar sikari? Cutar sikari bata da magani- amma ana iya rayuwa da ita A cewar hukumar kiyayye cututta ta Amurka , ciwon sikari nau’i na 2 yafi kama mutane yan shekaru 45 zuwa sama, amma ana samun ƙananan yara da matasa da ka iya kamuwa da cutar. Daga cikin abubuwan da ke jawo barazanar kamuwa da cutar sun haɗa da samun cutar a cikin zuri’a, yawan shekaru, ƙwayoyin halitta, ƙiba da rashin motsa jiki a cewar hukumar lafiya ta duniya. Africa Check ta tuntuɓi wani farfesa akan magunguna da cututtakan na Jami’ar Benin Aihanuwa Eregie akan batun. A wannan lokacin babu maganin ciwon sikari, a na dai kawai kula da masu cutar ne. Akwai daidaita abun da za’a ci wanda ya haɗa da cin abincin da ya dace sai kuma motsa jiki kamar yadda likitoci suka umarta. Akwai kuma magunguna kala kala da suka haɗa da ƙwayoyin magani da allurai, da za’a ringa amfani da su don dai daita yawan sikari a jiki, duk hakan ya danganta da nau’in ciwon da mutum ke ɗauke da shi, Eregie ya faɗa. Eregie ya ce waɗannan maganganu da haɗe haɗe zasu iya sa marasa lafiyan da suka daina shan magani su ƙare a asibiti da wata matsalar matsananciya. Africa Check ta taɓa tantance makamanciyar wannan da’awar . Kamar dai waɗancan da’awowin haɗin albasa, shuwaka da zuma basa maganin ciwon sikari nau’i na 1 da na 2. Gwajin jini ne kawai zai tabbatar da ko mutum na ɗauke da cutar da irin nau’in da ya ke ɗauke da shi, kuma masana sun bada shawarar yin gwajin sikari lokaci zuwa lokaci.
(sw)
|