?:reviewBody
|
-
A TAƘAICE: Babu hujjar cewa Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar All Progressives Party, ya ce hukumar zaɓe bata da ƙarfin da zata hana ƴan ƙasa da shekaru 18 yin zaɓe, ko cewar su ne waɗanda ke da ƴancin yin zaɓe. Wani babban ɗan siyasa ya ce, hukumar zaɓen Najeriya bata da ikon hana ƴan ƙasa da shekaru 18 yin zaɓe a zaɓen ƙasa mai zuwa. Wannan na cikin wasu kalamai da ke ta yawo a Facebook tun farkon watan Janairun 2023. INEC ba ta da ƙarfin da zata hana waɗanda shekarun su basu kai ba yin zaɓe, duk zasu kaɗa kuri’a a matsayin su na ƴan ƙasa masu ƴancin yin zaɓe, a cewar kalaman. An alaƙanta kalaman ga shugaban APC. Ana nufin Abdullahi Adamu , shugaban jam’iyyar All Progressives congress . Ƴan Najeriya na shirin zaɓen sabon shugaban ƙasa, da gwamnonin jihohi da ƴan majalisa, a watannin Fabrairu da Maris. A cewar Inec, wato hukumar zaɓe mai zamankanta ta ƙasa , ƴan ƙasar da ke ƙasa da shekarun da aka amince ayi zaɓe na 18, ba za’a barsu su yi rijistar zaɓe , yin zaɓe ko kaɗa kuri’a ba. Shin Adamu ya faɗi hakan? Mun bincika. Babu labaran da ya kawo rahoton wannan sanarawa mai tunzurarwa Furucin bai nuna waje da lokacin da Adamu ya faɗa ba. Babu kuma wani gidan jaridar da ya ruwaito shi yana faɗar wani abu makamancin yin zaɓen waɗanda shekarun su basu isa yin zaɓen ba. Idan da Adamu yayi wannan sanarwa mai tunzurarwa da an samu sahihan gidajen jaridar da suka ruwaito. Kalaman ƙarya ne. A tsarin dokoki da hanyoyin yin zaɓe na Inec, akwai hukunci ga waɗanda shekarunsu basu kai ba, ƴan ƙasar waje, ko masu zuwa da sunan wani don yin zaɓe. Ba kawai za’a hana su yin zaɓen ba ne, za’a iya kamasu a kuma gurfanar da su gaban shari’a.
(id)
|