PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-08-20 (xsd:date)
?:headline
  • Shugaban kamfanin Pfizer yayi allurar rigakafin Covid- tsohon bidiyo ne da ba shi da nasaba da hakan (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • SHUGABAN PFIZER BAI YI ALLURAR RIGAKAFI BA. Wannan shine taken wani bidiyo da aka yi da manyan haruffa aka saka a TikTok aka kuma yaɗa a Facebook a Afrika ta Kudu a ranar 14 ga watan Agusta 2021. Bidiyon na ɗauke da tattaunawar da akayi da Albert Bourla , shugaban kamafanin haɗa magunguna da ke Amurka wato Pfizer , bidiyon dai ya ɗau tsahon daƙiƙa 30 ne kawai. Allurar rigakafi ta Pfizer-BioNTech an yi tane da haɗin gwiwar kamfanin biotechnology wato BioNTech na ƙasar Jamus. Tattaunawar cikin bidiyon na cewa Bourla bai yi allurar rigakafin ba, aka kuma tambaye shi lokacin da zai yi. Da zarar na samu dama, zan yi, a cewar sa . Abu na hankali a nan Meg, shine bana so na bada misalin mai tsallake layi. Ni ɗan shekaru 59 ne, ina da ƙoshin lafiya, bana aikin taimakon alumma. Don ba’a yiwa ire-ire na shawarar suyi allurar rigakafin. Sannan sai bidiyon ya sako wani bangare na fim ɗin iRobot na daƙiƙa 11, inda ɗan wasan ƙwaiƙwayo Will Smith yake atishawa kafin ya ce: A gafarce ni, bana son shirme. An dai saka bidyon a Facebook ne tare da tsokacin da ke cewa: As die CEOvan Pfizer nie die shot var nie! Wanda a harshen Afrikaans ke nufin: Idan shugaban Pfizer yaƙi yin allura! Saƙon ya samu masu kallo sama da sau 71,000 a cikin kwanaki biyar, inda akayi tsokaci har 4,300, sannan aka rarraba sau 6,400. Allurar rigakafi ta Pfizer-BioTech ɗaya ce daga cikin alluran rigakafin da ake da su- waɗanda suka haɗa da Johnson & Johnson da Oxford-AstraZeneca - waɗanda hukumar kula da kayan kiwon lafiya ta Afrika ta Kudu ta amince ayi amfani da su. Amma wasu ƴan ƙasar Afrika ta Kudu har yanzu basu amince su je ayi musu allurar rigakafin ba. Me bidiyon ya ƙunsa? Sannan shugaban Pfizer ya ki yin allurar? Bidiyon an yi shi ne lokacin ƙololuwar mace-mace sanadiyar Covid-19 a Amurka An ciro bangaren bidiyon na daƙiƙa - 30 daga wani bidiyo na mintuna uku ne, wanda shafin yanar gizo na hukumar watsa labarai ta CNBC ta fitar a ranar 14 ga watan Disemba 2020. Watanni takwas da suka gabata, dai dai lokacin da Amurka ta ke karɓar alluran rigakafin a karo na farko. Lokacin da Amurka ke cikin - ƙamarin cutar karo na biyu - wanda kawo yanzu shine mafi muni . A bidiyon na watan Disemba, Meg Tirrell babbar mai rahoto akan kiwon lafiya da kimiya ta CNBC ce ke wa Bourla tambayoyi. Bidiyon na da taken : Shugaban Pfizer Albert Bourla akan ƙin allurar rigakafi: ‘A yarda da kimiyya’ . A cikin cikakken bidiyon , Bourla bai ce yana so ya tsallake layi ba gaban ma’aikatan da ke wa alumma hidima . Amma ya ƙara da cewa zaɓen Pfizer ya nuna cewa idan har shugaban kamfanin ya yi allurar rigakafin, mutane da dama zasu samu ƙwarin gwiwar yin allurar fiye da ace shugaban ƙasar Amurka ne ya yi. Da wannan a zuciya ta, ina neman hanyar da zanyi allurar, duk da cewa lokacin yi na bai yi ba, Bourla ya ce . Don nuna amincewa da kamfanin. Ina son masoya su samu damar da na samu Bourla ya karɓi allurar rigakafi ta Pfizer - BioNTech a karo na biyu ranar 10 ga watan Maris 2021. Da yake saka hotonsa a Twita lokacin da ake masa allurar, ya rubuta cewa : Ina murnar karɓar allurar rigakafin #COVID19 ta Pfizer/BioNTech karo na biyu. Babu abun da nake so fiye da masoya na ma da jama’ar duniya su samu irin wannan damar. Duk da cewa har yanzu da sauran tafiya, amma dai muna aiki tuƙuru don ganin cewa an ci galabar ƙwayar cutar. A wata tattaunawa da yayi da Axios a HBO , wani shirin al’amuran yau da kullum, Bourla ya tabbatar cewa ya karɓi duka adadin allurar rigakafi ta Pfizer. Ya ce ya jira lokacin sa na yin allurar ya yi, kuma yana jin yanzu ya samu ƴanci. Babu abun da nake so fiye da naga masoyana da jama’ar duniya sun samu damar da na samu. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url