?:reviewBody
|
-
Wani hoto da ke yawo a Facebook a Afrika ta Kudu da Najeriya yayi gargaɗi ga masoya biskit. Yayi iƙirarin cewa an shigo da biskit ɗin da ake kira crunches daga Afrika ta Kudu zuwa Najeriya, kuma har ya kashe mutane 45. Yana ɗauke da sinadari mai guba. Hoton wanda aka aikowa shafin WhatsApp na Africa Check a watan Fabrairu 2022, ya haɗa da hotunan biskit, hoton yaro wanda duk jikin sa ɗauke ya ke da ƙuraje da kuma hoton kan mutum mamaye da wani abun kamar kuraje. Rubutun da ke jikin hoton ba shi da alaƙa da cin biskit da kuma hotunan da ke jikin hoton, ga abubuwa a azahiri- waɗannan biskit zasu iya kisa! Amma hakan da gaske ne? Biskit ɗin Crunch Cream ba a Afrika ta Kudu aka yi shi ba Rubutun da ke jikin hoton ya ce biskit din da ake kira crunches har da bada shawarar a binciko crunches biscuits a google, ya kuma nuna fakicin biskit ɗin Cream Crunches na kamfanin Fox. Ma’aikatan mu da ke Afrika ta Kudu sun bayyana rashin sanin wannan biskit mai suna Fox. Wannan ya fara tabbatar mana da kokwanton da muke akan da’awar. Da muka duba sunan biskit ɗin a google, ya bayyana mana biskit mai suna Golden Crunch Creams na kamfanin biskit na Fox ɗan asalin ƙasar Biritaniya. Duk da cewa za’a iya shigo da biskit Najeriya daga Biritaniya ta Afrika ta Kudu amma shigo da mai ƙunshe da guba zai yi wuya. Mutanen Afrika ta Kudu sun saba cin bisket ɗin alkama da ƙwaƙwa da ake kira crunches . Amma nasu a gida ake sarrafa shi yadda kowanne iyali ke son sa, don haka fitar da shi zuwa wata ƙasar zai yi wuya. An samo hoton daga wani shirin gidan talabijin Sai kuma muka yi kokarin bibiyar sauran hotunan da su ke tare da ainihin hoton . Da farko mun nemi hoton yaro mai ɗauke da ƙuraje duk a jikin sa da kuma hoton kai mai cike da ƙuraje da aka manna a jikin hoton, ba mu samu komai ba. Yayin da muka ciro hoton kan shi kaɗai muka duba shi sai muka samo wasu hotunan kan waɗanda suka fi fitowa , sai dai kuma wannan hoton kai ne a cikin hakoran ɗan adam masu tarin yawa. An rarraba hoton da dama a yanar gizo da taken da ake fatan zai bada dariya, wanda ake zaton iyaye zasu nuna wa ƴaƴan su idan sun buƙaci ganin yadda aljannar hakori ta ke. (Gargaɗi: Wannan zai iya jawo mummunan mafarki. ) Da muka cigaba da bincike a yanar gizo sai muka gano hoton na wani shirin wasan kwaikwayo ne mai dogon zango a tashar talabijin ta Channel Zero mai taken Candle Cove . Fuskar ban tsoron bata da alaƙa da cin biskit, ko cin crunchy ko wani abun. Ƙarya ce da aka jima ana yin ta Yanzu dai mun tabbatar gargaɗin bashi da alaƙa da hoton. Mun kuma dubo biskit ɗin crunches, kamar yadda saƙon ya umarta. Saƙon ya ce : Idan baku yarda ba ku bincika a google don samun ƙarin bayani akan ‘biskit ɗin crunches’ Ku ceci rayuka kamar yadda na cece ku. Duk wannan bincike ya kaimu ga gano wasu misalan wannan da’awar. Kamar misalin rarraba shi da aka yi a wani wajen rarraba saƙonni na Najeriya, da kuma inda aka rarraba yadda ake haɗa biskit ɗin crunches . Mun gano saƙon dai wata jaridar Afrika ta Kudu ta Northern Natal News ta taɓa tantance shi a matsayin labaran ƙarya a shekarar 2016. Jaridar ta fayyace kamar haka:Babu gubar da ke kashe jama’a a biskit ɗin crunches. A shekarar 2019 ne shafin yanar gizo na SYY Hoax Analyzer ya bayyana da’awar a matsayin ƙarya. Wannan da’awar an fara yaɗata a shekarar 2016, kuma har yanzu dai ƙarya ce.
(id)
|