PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2023-01-10 (xsd:date)
?:headline
  • Kira akan sanarwar ɗaukan ma’aikatan wucin gadi na INEC da ke yawo ta bogi ce (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • A TAƘAICE: Duk da cewa saƙonni na cigaba da yaɗuwa a kafafen sada zumunta a Najeriya, hukumar zaɓe ba ta ɗaukar ma’aikatan wucin gadi don aikin babban zaɓen 2023. An tabbatar: Inec zata ɗauki ma’aikatan wucin gadi guda miliyan 1.4, cewar wani saƙo da aka saka a Facebook a ranar 27 ga watan Disemba. Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriy a ko Inec, na ɗaukar ma’akaita kafin babban zaɓen ƙasar mai zuwa, wanda za’ayi a watannin Fabrairu da Maris 2023. Wani rubutun da aka wallafa a Facebook na cewa , Ku cike gurbin samun aikin Inec na wucin gadi na babban zaɓen 2023. Kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 ne ya ƙirƙiri hukumar zaɓe mai zamankanta ta ƙasa (INEC) wadda ayyukan da zata yi suka haɗa da tsara zaɓe ta hanyar ofisoshin zaɓe a ƙasar. Shin Inec na ɗaukar ma’aikata? Mun bincika. Ɗaukar aiki na ƙarya A ranar 3 ga watan Janairu 2023, Inec ta wallafa a Facebook cewa kiran neman aikin, ƙarya ne. Ya kamata jama’a su gane cewa hukumar bata ɗaukar ma’aikatan wucin gadi na babban zaɓen 2023. An rufe wajen ɗaukar ma’aikatan wucin-gadi na yanar gizo a ranar 14 ga watan Disemba 2022, rubutun da hukumar ta wallafa a Facebook, ke cewa . A wata sanarwa da Rotimi Oyekanmi ya sawa hannu, shugaban watsa labarai na Inec, ya ce , an buɗe wajen ɗaukar ma’aikata a yanar gizo daga ranar 14 ga watan Satumba zuwa 14 ga watan Disemba, a halin yanzu dai hukumar bata ɗaukar ma’aikata. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url