PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-02-12 (xsd:date)
?:headline
  • Haɗin garin namijin goro, zuma da citta basa maganin rashin ƙarancin maniyyi (tl)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani rubutu da ke ta yawo a wani shafin Facebook Nigeria Beauty & Health Arena yana ikirarin cewa haɗin garin namijin goro, zuma, garin citta da ruwa yana magance matsalar ƙarancin maniyyi ko azoospermia. Rubutun ya bayyana yadda za’a yi haɗin da yadda za’a sha, tare da ƙare bayyanin da cewa; a rarraba wannan bayani a ko’ina a Facebook don a taimaka. Ina jiran shaidar ku. Ubangiji yayi albarka. Matsalar ƙarancin maniyyi da ake kira da oligospermia , itace lokacin da ɗigon milimita ɗaya na maniyyin mutum baya ɗauke da ƙwayoyin halittar maniyya da suka kai miliyon 15. Azoospermia shi ne lokacin da namji baya kawo maniyyi lokacin da ya kawo wajen saduwa. Abubuwan da ke jawo hakan sun haɗa da matsalar hormone, toshewar hanyoyin haihuwa, matsalar kawowar maniyyi yayin saduwa ko matsalar aiki ko halittar ƴa ƴan maraina. Shin akwai hujjar da ta tabbatar da wannan haɗin na gida na maganin matsalar? Mun bincika. ‘ Ana magance matsalar, amma a tuntuɓi likita’ Farfesa Sulayman Alege Kuranga masani akan matsalar mafitsara da ke tsangayar kimiyar kiwon lafiya na Jami’ar Ilorin da ke yammacin Najeriya, ya tabbatar da cewa wannan da’awar ba dai dai ba ce. Babu wata hujja a kimiyance da ta tabbatar da hakan. Idan wata cuta ce ke jawo ƙarancin maniyya zamu yi maganin cutar, hakan kuma zai taimaka, farfesan yace. Ya kuma ƙara da cewa akwai abubuwa da dama da suke jawo ƙarancin maniyyi da azoospermia. Akwai kuma magungunan su dai dai da abun da ya jawo matsalar. Kuranga ya ce hanya mafi dacewa ga mazan da ke fama da matsalar shi ne suyi ƙoƙarin ganin ƙwararru a fannin don basu maganin da ya dace bayan sun yi gwaje gwajen da suka dace. Africa Check ta taɓa tantance makamanciyar wannan da’awar da ke cewa haɗin kayan itatuwa na maganin rashin haihuwa da wasu matsalolin da suka danganci kiwon lafiya. Kamar dai waccan da'awar wannan ma ƙarya ce. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url