PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-07-27 (xsd:date)
?:headline
  • Shafa ƙugu baya ƙara yawan maniyyi (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Shafa tsakiyar ƙugu na sa ƙarin ruwan maniyyi, a cewar wani hoto a Facebook wanda mutane da dama suka aka rarraba shi. Hoton na ɗauke da kanun rubutun kamar haka, Yawan maniyyi da kuma hoton babban ɗan yatsa akan tsakiyar ƙugu. Ku ƙara yawan maniyyi ta hanyar shafa nan wajen a ƙugun ku, aka rubuta akan hoton . Wasu da su ke tsokaci a ƙasan rubutun waɗanda suka kai sama da mutum 600 , na neman a tabbatar musu da gaskiyar batun. Akwai wata hujja a kimiyyance? Menene ƙarancin ruwan maniyyi? A cewar Mayo Clinic , wata cibiyar kiwon lafiya mallakar Amurka, ana ƙirga yawan maniyyin namiji ne ta hanyar dubawa da madubin dibarudu, sannan a ƙirga yawan ƙwayoyin halittar maniyyin da suka bayyana. Yawan ƙwayoyin halittar maniyyin lafiyayyen mutum yana kamawa daga miliyan 15 zuwa sama da miliyan 200 kowanne milimita. Wannan na nufin ƙasa da miliyan 39 yayin inzali. Babu hujja a kimiyyance Wannan ai abun dariya ne, duk shekarun da nayi ina aikin kiwon lafiya ban taɓa jin haka ba, Cewar Sulyman Kuranga, Farfesan mafitsara na jami’ar Ilorin da ke arewa ta tsakiya a Najeriya, kamar yadda ya shaidawa Africa Check. Ya ce: Babu wata hujja a kimiyance cewa wannan zai ƙara yawan maniyyi. Sau tari ƙwayoyin cuta ke jawo matsalar ƙarancin yawan maniyyi. Idan an magance cutar, yawan maniyyi namiji na dawowa dai dai. Don haka shafa ƙugu baya ƙara yawan maniyyi. Babu hujjar da ta tabbatar da hakan a kimiyance, hakan bashi da nasaba da samuwar ruwan maniyyi, Kuranga ya ce. Bamu samu wani bayani ko bincike da akayi akan hakan ba. Africa Check ta taɓa tantance wata da’awa makamanciyar wannan, wadda ke cewa haɗa wasu magungunan gargajiya na ƙara yawan maniyyi. Kamar dai wannan su ma ba mu samu wata hujja a kimiyyance ba, don haka da’awar ƙarya ce. (so)
?:reviewRating
rdf:type
?:url