PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-07-27 (xsd:date)
?:headline
  • Babu wata cikakkiyar hujjar cewa jiƙaƙƙen ganyen mangwaro na taimakawa masu cutar suga nau’i na biyu (sw)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani saƙo da ke yawo a Facebook a Najeriya na iƙirarin cewa za a iya amfani da ganyen mangwaro don kula da cutar suga nau’i na biyu. Rubutun na Facebook na cewa : Ganyen Mangwaro na ɗauke da sindarin tanins da antosiyanis waɗanda suke da ikon taimakawa jiki ya samar da sinadarin insulin, ya daidaita yawan suga a jiki, ya taimakawa mai cutar suga nau’i na 2. Yana taimakawa mai ciwon rage alamomin ciwon a jiki, kamar yawan fitsari da daddare, ya kuma yi maganin cutukan sugan da akafi sani da aniyofati da ratinofati. Ciwon suga cuta ce da ake rayuwa da ita a jik i, wacce ke haddasa hauhawar sikarin da ke jiki. Saboda gazawar jiki wajen samar da isasshen sinadarin insulin , ko kuma baya amfani da insulin ɗin da jiki ke samarwa yadda ya kamata. Jiki na amfani da sinadarin insulin wajen sarrafa suga da kitse. Cutar suga nau’i na 1 na afkuwa ne lokacin da jiki baya iya samar da isasshen sinadarin insulin , yayin da cutar suga nau’i na 2 na afkuwa ne lokacin da jiki ya gaza amfani da sinadarin insulin. Rubutun na Facebook ya bayyana yadda za’a haɗa da kuma yadda za’a yi amfani da jiƙon ganyen mangwaron. Shin akwai hujja a kimiyyance da ta tabbatar da hakan? Mun bincika. ‘Ba zan bawa kowa shawarar ya sha haɗin ba’ - cewar ƙwararre a fannin. A duk duniya, kimanin mutane miliyan 400 ke fama da cutar suga . Da dama sun fito daga ƙasashe masu ƙarancin tattalin arziƙi. Cutar na kashe aƙalla mutane milyan 1.6 a kowacce shekara, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana. Wasu binciken sun tattara bayanai akan sinadarin yaƙi da cutar suga da ke jikin mangwaro. Sharhi akan ayyukan ɗa itace da ganyen mangwaro wajen magani ya nuna cewa zai iya zama yana cikin magungunan maganin cutar suga. Wasu daga cikin waɗannan itatuwa na da abubuwa kala kala a jikin su masu amfani, Aihanuwa Eregie, Farfesa akan magunguna ta jami’ar Benin da ke kudu maso yammacin Najeriya ta shaidawa Africa Check. Zan fi so ace anyi binciken waɗannan abubuwan a kimiyance, a fitar da abu mai amfani a yi gwaji akan sa na ɗan lokaci. Amma yanzu ba zan bawa kowa shawarar ya sha wannan haɗin ba, Farfesar ta ce. Ta ƙara da cewa: Duk likitan da ya samo cikakken horo akan cutar suga, ba zai ce a sha ganyen mangwaro ba. Hukumar kula da cututtaka masu yaɗuwa ta Amurka ta ce, za’a iya rayuwa da cutar suga tare da cin abincin da ya dace da shan magunguna don sauƙaƙa cutar suga, hawan jini da yawan kitse. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url