PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-10-18 (xsd:date)
?:headline
  • Ba haka ba ne, furen St John’s wort da barasa basa maganin ƙurajen herpes (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Na sami saƙo ta dm daga wata mace da take fama da barkewar ƙurajen gaba, wani saƙo a Instagram ya fara da cewa. Sai kuma ya bada magani: Furen St John’s wort da barasa. St John’s wort wani haɗin itatuwa ne da ke da maganin yaƙi da ƙwayar cuta wanda zai taimakawa masu fama da matsalar ƙurajen gaba, saƙon ya ce . Wannan magani ne da ake haɗawa da barasa, kuma ana barinsa ya jiƙu har tsahon makonni 6, sai a tace a sha. Za’a iya amfani da barasar 80 proof vodka ( kamar Smirnoff ice vodka ) wajen haɗawa. Saƙon na tare da bidiyon yadda za’a yi haɗin. Menene ƙurajen herpes ? Ƙurajen herpes cuta ce da ƙwayar cuta ta herpes simplex ke jawowa. Ƙwayoyin cutar iri biyu ne. HSV-1 tana jawo ƙuraje a baki misalin huciyar zazzaɓi , kuma ana yaɗa ta daga baki zuwa baki. Ƙurajen gaba kuma ƙwayar cutar herpes HSV-2 ce ke je jawo shi, duk da cewa HSV-1 ma tana iya jawowa. Matuƙar aka kamu da su ƙwayar cutar na zama a jiki har abada, amma dai basa nuna wasu alamu a jiki. Shirin kula da lafiya na National Health System na Britaniya ya ce, a inda aka samun alamun herpes na bayyana a gaba za’a samu ƙananan ƙuraje ne ke fitowa waɗanda suke fashewa su bar jan buɗaɗɗen tabo a gaba, dubura da matse-matsi; suna sa gaban zafi da ƙaiƙayi; jin zafi yayin yin fitsari da kuma fitar da ruwa ga mata. Idan ba’a yi maganin alamun ba zasu iya zama barazanar kamuwa da cutar HIV ga wanda ya ke fama da su. Furen St John’s wort ( wanda a kimiyance akafi sani da Hypericum perforatom ) itace ne da ya samo asali daga Turai yana kuma fitowa a daji. An daɗe ana amfani da shi wajen maganin matsananciyar damuwa . Amma masana sun yi gargaɗin cewa yawon amfani dashi ka iya rage ƙarfin magungunan asibiti, kamar magungunan cutar HIV dana sankara. Shin jiƙa furen a cikin barasa zaiyi maganin ƙwayar cutar herpes? A guji zafi kuma kar a wanke gaba da wasu sinadarai Haɗin furen St John’s wort da barasa bai tabbata ba wajen maganin cutar herpes, Dr Olajumoke Ogunro , likitar mata ta asibitin haihuwa na Alpha Assisted Reproductive Klinic da ke Lagos ta shaidawa Africa Check. A halin yanzu babu maganin herpes. Ta ƙara da cewa akwai wasu abubuwan da za’a iya yi a gida don rage alamun cutar kamar ƙaiƙayi da raɗaɗi. Kar ku shiga cikin zafi sosai ko cikin zafin rana mai yawa. Gujewa wanke gaba da kayan kula da gaban mace zai taimaka matuƙa, Ogunro ta ce. Likitar ta gargaɗi cewa St John’s wort na iya jawo babbar matsala idan ta haɗu da wasu magunguna. Wasu ƙasashen sun haramta amfani da furen, yayin da wasu ƙasashen ke duba yiwuwar hana amfani da shi. Kar ku bar alamun ciwo baku nemi magani ba Idan kuna zaton kuna fama da alamomin herpes, ku nemi ganin likita don baku maganin da ya dace don magance alamomin. Idan ba ku sha magani ba zaku iya cigaba da samun cutar akai akai, duk da dai hakan ba kasafai take faruwa ba, Ogunro ta ce. Idan baku nemi magani ba za’a ɗau tsahon lokaci kafin alamun su ɓace. Haka nan cutar na iya yaɗuwa idan ba’a magance alamun ba. Idan kuka taɓa ruwan da ƙurjin ke fitarwa kuka taɓa wani sassa na jikin ku, zaku yaɗa cutar a wani sashe na jikin ku. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url