PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-10-19 (xsd:date)
?:headline
  • Hoton titi a Pakistan ne, ba titin Ughelli-Asaba da ake aiki a Najeriya ba ne (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • ATAƘAICE : Wani hoton na ta yawo a Najeriya. Wanda ke cewa aikin babban titin Ughelli da Asaba da ke jihar Delta ne da aka kammala, aka kuma ɗora alhakin ginin titin ga gwamnan jihar Ifeanyi Okowa. An yi haka ne don a ƙara fito da gwamnan, saboda takarar shugabancin ƙasar da ya ke son yi a zaɓen 2023. Hoton, na wani babban titi ne a Pakistan ba Najeriya ba. An saka wani hoto a wani guruf na Facebook Najeriya a watan Satumba 2022 da ke iƙirarin cewa babban titin Ughelli zuwa Asaba da ke jihar Delta , kudancin Najeriya ne aka kammala. Taken da ke tare da hoton na cewa ; ‘Mun gode gwamna Ifeanyi A. Okowa da gaggawar saka hannu da kayi da kuma kammala aikin babban titin Ughelli-Asaba a ƙasa da shekaru 8 da fara aikin ka na gwamna. Asaba itace babban birnin jihar Delta, yayin da Ughelli kuma wani gari ne mai nisan kilo mita 170 daga kudu maso yamma. Ifeanyi Okowa shi ne gwamnan jihar kuma ɗan takarar kujerar mataimakin shugaban ƙasa daga jam’iyyar People’s Democratic Party a zaɓen Najeriya na 2023. Rubutun na Facebook ya haɗe da shafin gwamnan na Facebook . Aikin babban titin mai ɗauke da hanyoyi biyu, gwamnatin da ta gabata ce ta fara shi ƙarƙashin gwamna Emmanuel Uduaghan a shekarar 2007. Amma an bada umarnin kammala aikin titin a shekarar 2019 ƙarƙashin gwamnatin Owowa. An sake rarraba hoton tare da da’awar a nan , nan da nan . Shin hoton da aka rarraba a shafukan sada zumunta na titin Ughelli-Asaba ne da aka kammala? Mun bincika. Hoton titin motoci na Hazara ne da ke Pakistan Binciken hoton da kafar tantance hotuna ta Google reverse image search ya kai mu matattarar wasu hotuna da aka tattara ranar 20 ga watan Satumba 2020 a shafin Pinterest wanda wani shafin yanar gizo na tafiye-tafiye na Pakistan suka saka. A wajen an nuna hoton a matsayin hoton titin motoci na Hazara a ƙasar wadda ke Kudancin Asia wato Pakistan . Da kuma muka binciko ruwan sama a titin motoci na Hazara, binciken ya kai mu ga hotunan wannan titin , wanda aka bayyana a matsayin titin mota na Hazara. An fara aikin titin mai tsahon kilomita 180 a shekarar 2014, an kuma gama ginin aka kuma ƙaddamar da shi a tsakiyar 2020 A watan Fabrairun 2022, Nigerian news ta kawo rahoton zanga-zangar da masu bin titin Ughelli- Asaba sukayi don kokawa da yadda aka ƙi gyara titin. Amma bamu samu wani sabon rahoto akan aikin titin ba, ko rahoton cewa an kammala aikin titin. Hoton da ke yawo a kafafen sada zumunta a Najeriya ba ya ɗauke da hoton titin Ughelli-Asaba, kuma ba a Najeriya aka ɗauki hoton ba. Ba’a kammala babban titin Ughelli da Asaba da ke jihar Delta ba. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url