PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-01-29 (xsd:date)
?:headline
  • Masu fafutukar Biafra sun kori Fulani a jihar Ebonyin Najeriya? Ba haka bane bidiyon da ya nuna makiyayan na tafiya sun tafi ne bisa ra'ayin kansu (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani bidiyo da ke ta yawo a yanar gizo a farkon watan Junairun 2021 na nuna wata ƙatuwar motar ɗaukar kaya ajiye a gefen wasu gidajen kara, wasu daga cikin gidajen ana ƙoƙarin ciccire su daga ainihin yadda su ke. Wadannan Fulani ne da ke jihar Ebonyi, za'a ji wata murja na faɗa . Mun tarwatsa dukiyoyinsu, sannan mun fatattake su tare da dukiyoyin su. Jihar Ebony i da ke Kudu maso gabashin Najeriya na da ƴan kabilar Igbo masu tarin yawa . Fulani waɗanda mafi akasarin su Musulmi ne makiyaya, na warwatse a Afrika ta yamma. Ba ma buƙatar Fulani a jihar Ebonyi, muryar ta cigaba da cewa. Ba ma buƙatar Miyetti Allah a jihar Ebonyi. Ƙ ungiyar makiyaya ta Miyetti Allah , ƙungiya ce don bada shawara ga Fulani makiyaya a Najeriya. An wallafa bidiyon a shafin Facebook da kuma YouTube tare da cewa hanyar samar da tsaro ta gabas (ESN) sun kori Fulani daga matsuguninsu a jihar Ebonyi. Nnamdi Kanu ne ya ƙirƙiri hanyar a watan Disembar 2020. Nnamdi Kanu shi ne shugaban masu fafutukar ƴankin Biafra , wanda ke ta haƙilon a ware gabashin Najeriya ya zama mai cin gashin kansa. Kanu ya ce an ƙirƙiri ESN don a fatattaki yan ta'adda da ta'addanci da kashe kashen ba gaira ba dalili a yankin kuma ita ce zatayi mana maganin matsalar tsaro da ta'addancin Fulani. An sake wallafa bidiyon da hotunan , ana kuma ta tsokaci kamar haka ƴan hanyar samar da tsaro ta gabas ba da wasa suke ba.......... Fulani na tattara inasu inasu, ƙabilar mugaye wani taken kuma na cewa ESN akan aiki yayin da ta kori Fulani makiyayi daga dazukan jihar Ebonyi. Akwai rahotannin da ke cewa ana azabtar da Fulani makiyaya a jihar Ebonyi, har an samu makiyayen sun shaidawa BBC Hausa a 2020 cewa a ƙalla jama'ar su 21 aka kashe aka kuma ƙone gidajensu. Shin da gaske ana aikata wani abu makamancin abun da bidiyon ya ƙunsa? Mun bincika. ‘ Komawa jihar Taraba’ A ranar 4 ga watan Junairu gwamnatin jihar Ebonyi tayi t aron manema labarai inda tayi Allawadai da tsoro da tashin hankalin da bidiyon ya jawo, ta kuma bada umarnin a cafke waɗanda ke yaɗa bidiyon. Jaridar Guardian ta Najeriiya ta ruwaito cewa Inusa Sani sakataren kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Ebonyi ya bayyana bidiyon a matsayin labaran ƙarya ne da wasu suka ƙirƙira don hana zaman lafiya. Abun da ya faru shine a ranar 2 ga watan Junairu ɗaya daga cikin mu Alhaji Adamu, wanda ke zaune a ƙauyen Ozibo a Nkaleke Ichaba/Enyibishiri ya sanar da ƙungiya cewa zai koma jihar Taraba da zama, abunda jaridar Guardian ta ruwaito Sani na cewa. Babu wani makiyayi da aka kaiwa hari ko aka kora daga jihar Ebonyi. Ya ƙara da cewa Fulani da jama'ar jihar na zaune lafiya da juna babu tsoro, tsoratarwa ko cin zarafi daga junan su. Rundunar ƴansanda ta jihar tuni ta ƙaryata batun korar Fulanin. A ina aka samu tashin hankali Africa Check a kwanan nan tayi nazari akan yadda kafofin ƴada labaran masu fafutukar yankin Biafra ke ta ƴada ƙirƙirarrun labarai a matsayin na haƙika . Mun jima muna tantance ire iren waɗannan da'awowi da dama, da yawan su ba'a cika ƙaidar rubutu wajen rubuta su. Basu da madogara, sannan suna amfani da bidiyo ko hotunan da aka sauya daga ainihin yadda suke. Babu hujjar da ta nuna cewa ESN ta kori jama'ar daga jihar Ebonyi. Ana iya gani a bidiyon yadda Fulanin ke tafiya cikin ƙwanciyar hankali. Za'aga mutane na ta kaiwa suna kawowa, wasu na tsaye suna hira, ana kuma kin muryoyin yara suna wasa. Babu alamun tashin hankali ko damuwa ko jami’an ESN na korar su. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url