PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-08-22 (xsd:date)
?:headline
  • Hukumar kula da kaɗaɗen shiga ta ƙasa bata ɗaukar ma’aikata (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani saƙo da aka saka a Facebook Najeriya na iƙirarin cewa hukumar kula da kuɗaɗen shiga ta ƙasa, wadda akafi sani da Firs na ɗaukar ma’aikata na shekarar 2022-23. Sakon na cewa : FIRS sun fara ɗaukar ma’aikata na shekarar 2022/2023. Saƙon ya bayyana hanyoyin da ya kamata ku bi don taimaka muku ku samu sunan ku ya fito a cikin shirin ɗaukar ma’akatan hukumar kula da kuɗaɗen shiga na bana. Sannan aka bada wani wajen latsawa da mutum zai latsa ya shiga, don ƙarin sanin cikakken bayanin yadda za’a nemi aikin. Mun samu da’awowi makamantan wannan, wanda wajen latsawar ke kai mutum wani shafi na daban , a nan da nan . Firs ce ke da alhakin tarawa, shigarwa da lissafa kuɗaɗen haraji da sauran kuɗaden shiga na Najeriya, ƙasar da tafi kowacce ƙasa girman tattalin arziƙi a Afrika. Shin suna ɗaukar ma’aikata? Ba’a ɗaukar ma’akata a hukumar kula da haraji Babu hujjar da ta nuna cewa ana ɗaukar ma’aikata a shafin hukumar na yanar gizo , shafin su na Tiwita ko shafin su na Facebook . A ranar 1 ga watan Agusta Firs ta wallafa wata sanarwa a shafukanta na Tiwita da na Facebook , suna gargaɗin jama’a akan su kiyayi ƴan damfara, sannan suka ce basa ɗaukar ma’aikata. Hukumar na son ta jaddada cewa bata ɗaukar ma’aikata a halin yanzu, sannan bata taɓa ɗaukar ma’aikata ta bayan gida ba, sanarwar ta ce . Ta kuma gargaɗi gidajen jarida da su guji wallafa shafuka ko sanar da hanyar neman aiki wadda hukumar bata da masaniya akai, ko kuma waɗanda suka kasance na bogi a shafukan su. (so)
?:reviewRating
rdf:type
?:url