?:reviewBody
|
-
Wan i hoto da ya yawan masu kallonsa ya haura miliyan 4 tun lokacin da aka ɗora shi a Facebook a ranar 8 ga watan Janairu 2021, yayi iƙirarin cewa takunkumin rufe fuska zai iya jawo lalacewar ƙwaƙwalwa da ƙwayar bakteriyar da ke jawo cutar Nimoniya, ya hana sinadarin oksijin shiga jiki ko sassan jiki. Hoton na haɗe da wani hoton rubutun wata jarida. Rubutun na da taken Takunkumin rufe fuska na jawo ‘lalacewar ƙwaƙwalwa’ a cewar likitan lafiyar ƙwaƙwalwa. Rubutun da ke saman hoton na cewa saka takunkumin rufe fuska zai hana ku shaƙar isashshiyar oksijin, zai sa ku shaƙi dattin da jikin ku ya ke fitarwa, zai kuma jawo muku ƙwayar cutar Nimoniya wadda zama da takunkumin a fuska na lokaci mai tsaho ke jawowa. Ko yaya gaskiyar hakan? Ko takunkumin na da hatsari ga lafiyar mutum? Takunkumin rufe fuska baya hana jiki samun oksijin Rubutun da aka yi amfani da shi a hoton an ɗauko shi daga jaridar Light da ke ƙasar Ingila, wadda ta ke kiran kanta da jaridar gaskiya. Jaridar ta ruwaito cewa wata likita Margarite Griesz-Brisson ta ce ba tare da bada wata hujja ba, cewa sa takunkumin rufe fuska zai ba tare da wata tantama ba jawo ƙarancin oksijin da yawan kabon dioxide. Likitar ta ce, jijiyoyin ƙwaƙwalwa bazasu rayu ba tare da oksijin ba, kuma rashin oksijin zai iya jawo lalacewar ƙwaƙwalwa da sassan jiki. An jero waɗannan da’awa a hoton na Facebook, amma babu hujjar da ta tabbatar takunkumin na jawo ƙarancin oksijin a ƙwaƙwalwa. Africa Check ta taɓa tantance da’awa makamanciyar wannan kamar yadda wasu masu tantance labarai sukayi. Likitoci da jami’an kiwon lafiya sun ce saka takunkumin rufe fuska ba shi da hatsari, haka nan itace hanya mafi inganci wajen kiyaye yaɗuwar Covid-19. Takunkumin rufe fuska baya sa mu shaƙi datti Hukumar lafiya ta duniya ta ce, ɗaukar dogon lokaci da takunkumin a fuska na takurawa, kamar yadda jami’an lafiyan da ke amfani da ita na lokaci mai tsaho suke faɗa. Amma sa takunkumin na lokaci mai tsaho baya sa saƙar guba ko ƙarancin oksijin. Masana a wani shiri da ake kira teburin kiwon lafiya , wanda ƙungiyar fasaha da aikin jarida meedan ta ƙirƙira na cewa : iƙirarin da ake na cewa, amfani da takunkumin rufe fuska na lokaci mai tsaho na iya jawo ƙarancin iskar oksijin, jiri da wasu ƙalubalai ga kiwon lafiya, bashi da tushe a kimiyance. Ko takunkumin rufe fuska da jami’an lafiya ke amfani da shi, kamar N95 masu taƙaita iska basa jawo ƙarancin iskar oksijin ko su sa shaƙar carbon dioxide. Sai dai idan ana fama da wata lalurar mai tsanani, wanda abu ne mawuyaci . Farfesa Donald Milton na makarantar koyan kiwon lafiyar al’umma da ke jami’ar Maryland , ya taɓa shaidawa Africa Check cewa, baya sa ƙaruwar shaƙar iskar carbon dioxide kuma ya nuna mana hujjoji da dama da suka nuna cewa amfani da takunkumin rufe fuska yana taimakawa matuƙa wajen daƙile yaɗuwar Covid-19. Jami’an lafiya da dama sun nuna cewa saka takunkumin rufe fuska baya shafar yawan oksijin a jinin mutum. Wani likita mutumin Ireland ya nuna yadda yawan oksijin ɗin sa ya kasance dai dai duk da cewar ya saka takunkumin rufe fuska har guda shida, ɗaya akan ɗaya. Jaridar Light na yawan wallafa ra’ayoyin bogi da labaran ƙarya akan Covid-19 . Waɗanda suka haɗa da da’awar da ba a tantance ba da ke cewa, Bill Gates ya ƙirƙiri microchip kuma za’ayi amfani da shi a cikin allurar rigakafin don a ringa sarrafa tunani da kuma jikin ɗan Adam, da kuma labaran ƙaryar da cewa babu wanda aka keɓe akan cutar Covid-19, don haka babu cutar. An samar da ƙwayar cutar a watan Fabrairu 2020, akwai ma hotunan ƙwayar cutar da aka ɗauka da madubin duba ƙwayoyin cuta na musamman. Takunkumin rufe fuska baya jawo cuta- yana kiyaye ɗaukar ta Da’awar da ke cewa takunkumin na jawo ƙwayar cutar bakteriya ma ƙarya ce . An sha tantance da’awar, kamar yadda aka sha tantance da’awa da dama akan takunkumin rufe fuska na jawo wasu cututtukan . Hatta takunkumin rufe fuskar da ake yi da yadi ma yana daƙile yaɗuwar Covid-19, haka nan ƙwararru akan kiwon lafiya sun amince da ingancin su.
(id)
|