PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-10-20 (xsd:date)
?:headline
  • Antifasfaran diyodaran da ake shafawa a jiki don hana gumi da wari baya jawo cutar sankarar mama (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani saƙon a Facebook da za’a iya cewa na a mutu ko ayi rai na iƙirarin cewa antifasfaran diyodaran da ake shafawa a jiki don hana gumi da wari na jawo sankarar mama, musamman a kusa da hammata. Kaya da yawa a kasuwa na haɗe da antifasfaran diyodaran da ake shafawa don hana gumi da wari, saƙon ya ce . Diyodaran bashi da matsala amma ANTIFASFARAN, KUL. Yawan gubar da ke jiki na jawo hauhawar ƙwayoyin halitta: SANKARA. Saƙon na cewa jiki na fitar da guba lokacin da ake gumi, kuma jikin na iya yin hakan ne ta wasu wurare: bayan gwiwa, bayan kunne, ingilish eriya, da kuma hammata. Antifasfaran, zai hana ku gumi, don haka zai sa jiki fitar da guba daga hammata. Kuma gubar ba bacewa zata yi kawai ba. Saƙon ya ƙara da cewa wannan sinadari mai ɗauke da abu mai hatsari da ke cikin antifasfaran don hana gumi na ratsawa cikin jiki, musamman ga matan da ke aske gashin hammata. Antifasfaran da ake shafawa don hana gumi , yana rage gumi, musamman daga hammata. Daga cikin mahaɗin sa akwai aliminiyam wanda ke toshe ƙofofin gumi na ɗan gajeran lokaci. Sankarar mama mafi akasari ta fi kama mata , duk da cewa maza ma na iya kamuwa da ita. Shin antifasfaran da ake shafawa don hana gumi na jawo sankarar mama? An tantance sosai kuma a bayyane Africa Check ta tambayi Dr Leon Marais , likitan sankara a OnCoCare , cibiyar kula da ciwon sankara da ke Afrika ta Kudu akan wannan da’awar. Su dai likitocin da akafi sani da unkolojis sune waɗanda suka karanta cutar sankara suke kuma bada maganin ta. Cewar da akayi antifasfaran diyodaran da ake shafawa don hana gumi da hana wari na haddasa cutar sankara ‘an daɗe ana faɗar hakan’, likitan ya shaida mana. Likitan ya tura mu wani ‘babban shafin yanar gizo’ na ƙungiyar cutar sankara ta Amurka wanda shafin yayi rubutu akan wannan da’awar, ya kuma tantance ‘sosai kuma a bayyane’ akan cewar da’awar ƙarya ce . Akan kowacce takarda da ke cewa akwai alaƙa tsakanin antifasfaran da ake shafawa a jiki don hana gumi da cutar sankara, Marais ya ce, akwai kuma wata takardar da ke tabbatar da basu da alaƙa. Mun zanta da Farfesa Janet Poole , likitar cutar sankara a ƙananan yara ta asibitin karatu na Charlotte Maxeke da ke Johannesburg, Afrika ta Kudu. Likitocin sankara ga ƙananan yara sune suke bawa yara masu cutar sankara magani. Tayi watsi da wannan da’awa da ke cikin saƙon na Facebook, musamman cewa suna jawo sankarar mama kusa da hammata. Cewar da akayi ‘wurin’ da sankarar mama ke kamawa da kuma cewar amfani da antifasfaran duk shirme ne, Poole ta ce. Babu hujja a kimiyyance da ta tabbatar da alaƙar waɗannan abubuwa wajen kamuwa da sankarar mama. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url