?:reviewBody
|
-
A ranar 15 ga watan Fabrairun 2021 aka bayyana masaniyar tattalin arziki ƴar Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar babbar daraktar cibiyar kasuwanci ta duniya(WTO). Jimkaɗan bayan naɗin nata, wani hoton wata yarinya ya fara yawo a kafafen sada zumunta a Najeriya da cewa hoton sabuwar daraktar ce tana ƙarama. Wasu na yaɗa hoton tare da hoton babbar darakta na yanzu. Mun bincika ko wannan batu gaskiya. Hoton ya samo asali daga ƙasar Ghana tun 2014 Kafar tantance hoto ta Google reverse image search ta bayyana mana asalin hoton, wanda aka fara sa shi a yanar gizo a wani shafi mai suna Fresh Wall Street a shekarar 2014. Ta kuma nuna cewa hoton mai ɗaukar hoto Allen Coleman ne ya ɗauki hoton. Coleman ya shaida mana cewa ya ɗauki hoton a ƙasar Ghana a shekarar 2014, ya ƙara da cewa: Hoton na wata yarinya ce ƴar ƙasar Ghana. Babu abun da ya haɗa hoton da babbar daraktar WTO. Mun tambaye shi ko Okonjo-Iweala ce a cikin hoton, ya ce: Sam, ba ita bace. Africa Check ta sake bincikar hoton ta hanyar amfani da InVID WeVerfy . In da ta tabbata an ɗauki hoton a ranar 28 ga watan Juli 2014, aka kuma gyara shi kwana biyu bayan ɗaukar sa. Okonjo-Iweala dai an haife ta a ranar 13 ga watan Juni a shekarar 1954, shekarunta 60 a shekarar 2014.
(id)
|