PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-10-28 (xsd:date)
?:headline
  • Ƙasar Sin bata gina ofishin ƴan sanda a Najeriya ba, kuma bata karɓi ragamar ayyukan hukumar hana fasa ƙauri ba (tl)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • A taƙaice: Muhawara akan bashin da ƙasar Sin ke bin Najeriya na ta cigaba. Amma da’awar da ake cewa wannan babbar ƙasa ta yankin Asia na gina ofishin ƴan sanda a ƙasar da tafi kowacce ƙasa shahara a Afrika, har ma aka ƙara da cewa sun ɗau ragamar ayyukan hukumar fasa ƙauri ta Najeriya, bata da madogara. Ƴan’uwana ƴan Najeriya, shin kun san cewa tuni ƙasar Sin na gina ofishin ƴan sanda a Najeriya, sannan ƙasar Sin ta karɓi ragamar hukumar hana fasa ƙauri ta Najeriya? An nemar mana bauta ta dalilin bashi kenan. Wannan shine saƙon da ake ta kwafa ana mannawa a wurare daban-daban a Facebook a watan Oktoban 2022. Najeriya kwastam na nufin hukumar hana fasa ƙauri ta Najeriya . Alaƙar diflomasiya tsakanin Najeriya da ƙasar Sin ta samo asali tun shekarar 1971. Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaryata da’awar da ke cewa bashin ƙasar Sin ga Najeriya wani tarko ne. Sai dai jama’a na cigaba da muhawara akan basussuka da ƙasar Sin ke bin Najeriya . Gwamnatin ƙasar Sin ta gina ofishin ƴan sanda a Najeriya, kuma ta ɗau ragamar kula da fasa ƙauri? Mun bincika. Da’awar bata da wata hujja Babu ɗaya daga cikin sakonnin na Facebook da ya bayyana yadda da kuma inda aka samo labarin. Wannan rashin bayanai na nuna cewa da’awar ta ƙarya ce. Babu wani babban gidan jarida a gida da waje da ya ruwaito cewa ƙasar Sin na gina ofishin ƴan sanda ko karɓar ragamar kula da fasa ƙauri a ƙasar. Idan da gaskiya ne, da ya zama kanun labarai. Gidajen jarida na gida sun ruwaito cewa gwamnatin ƙasar Sin ta musanta da’awar cewa tana gina ofishin ƴan sanda a Najeriya. Binciken shafin gwamnatin ƙasar Sin na yanar gizo bai bamu wata hujjar da zata tabbatar da da’awar ba. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url