?:reviewBody
|
-
Maganin ƙarin girman kuturi da mazaunai na asali, ƙunshe a cikin wani saƙo da aka wallafa a Facebook. Saƙon ya cigaba da cewa, za'a haɗa garin itatuwan hulba, fanel, kumin, maaka a haɗa da man almon da man zaitun da zuma zasu ƙara girman kuturi da mazaunai. Saƙon ya ce mace zata sha haɗin bayan ta dafa , sannan ta shafa haɗin a maman ta da mazaunan ta. Shin abun haka ne a kimiyance? ‘ Idan ana bukatar ƙarin aje a ga likitocin da suka ƙware a wajen yin faskwarima’ Ƙwararru sun shaidawa Africa Check cewa kayan haɗin da aka ambata na da amfani a jikin ɗan adam amma babu wata hujja da ta tabbatar suna ƙarin da akace sunayi. Ga misali ya 'ya, ganye ko itacen hulba - ganye ne a rukuni daya da soya, ana kuma amfani dashi wajen ƙara dandanon girki - ana kuma daukar sa a matsayin magani . Hakanan ana amfani da yayan fanel wajen maganin cututtukan da suka danganci numfashi ko hanji . Farfesa Peter Olaitan na sashen ƙuna da faskwarima na jami'ar Ladoke Akintola ya ce, babu wata hujja a kimiyance da ta tabbatar da da'awar. Wannan duk shirme ne. Wannan haɗin baya ƙarin kuturi ko mazauna, a cewarsa. Olaitan wanda ya kasance likita ne mai fiɗa don yiwa halitta faskwarima ya ce ayi watsi da wannan da’awa, ya kuma shawarci matan da suke son yiwa halittar su faskwarima da su ziyarchi asibiti wajen ƙwararru a fannin. Jama’a na saka magunguna barkatai a kafafan sada zumunta don haka mu ringa kiyayewa , Olaitan ya faɗa. Africa Check ta tantance wata da’awa makamanciyar wannan wadda tayi iƙi'rarin haɗin ƙwai da man kaɗanya na gyaran mama.
(id)
|