PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-07-22 (xsd:date)
?:headline
  • Ba’a sauya lokacin yin zaɓen 2023 ba, kamar yadda wata da’awa a kafafen sada zumunta ke iƙirari (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bayyana ranar babban zaɓen 2023, wani rubutu da akayi a watan Julin 2022 a wani guruf na Facebook a Najeriya, wanda ke da mabiya har sama da 280,000 ya fara da cewa . Hukumar zaɓe mai zamankanta (Inec) itace ke da alhakin gudanar da zaɓe a Najeriya. Rubutun na iƙirarin cewa za’a gudanar da babban zaɓen 2023 da za’a zaɓi shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, ƴan majalisar wakilai da ƴan majalisar dokoki a ranar 18 ga watan Fabrairu 2023. Sannan za’a gudanar da na gwamnoni da ƴan majalisar jihohi a ranar 4 ga watan Maris 2023, rubutun ya ƙara da cewa. Mun ci karo da makamantan wannan da’awa a nan , nan da nan . Shin za’a gudanar da zaɓen Najeriya a wannan lokacin? Mun bincika. Babban zaɓen Najeriya zai kasance kamar yadda aka riga aka shirya A ranar 26 ga watan Fabrairun 2022 Inec ta wallafa jadawalin lokaci da abubuwan da za’a gudanar a babban zaɓen 2023 a shafinta na yanar gizo. Wannan na ɗauke da kwanan watan manyan al’amuran da za’a gudanar da zasu kai ga zaɓen kansa. Bayanan da aka wallafa sun nuna cewa za’ayi zaɓen shugaban ƙasa dana majalisa (wakilai da ta dokoki) a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023. Zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni zai kasance a ranar 11 ga watan Maris. Rubutun na Facebook bai bayyana lokaci ko dalilin da zai sa Inec ta sauya waɗannan muhimman lokuta a kalandar zaɓe ba. Mun duba shafin Inec na yanar gizo da shafukanta na kafafen sada zumunta ko zamu ga wajen da ta ambaci sababbin lokutan zaɓen, bamu samu komai ba. Irin wannan babban sauyi idan da gaske ne za’a samu manya gidajen jarida sun ruwaito. Bamu samu wata shaida da ta tabbatar da hakan ba. Irin waɗanna labaran ƙarya zasu iya saka masu kaɗa kuri’a ƙin zuwa su kaɗa kuri’a, su kuma shafi damar su ta shiga a dama a su a demokaraɗiya. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url