PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-07-20 (xsd:date)
?:headline
  • Babu hujjar cewa turara gaban ku yana da fa’ida a gare ku (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani rubutu a Facebook na iƙirarin cewa turaren yoni na iya magance tabon jikin tsokar jiki, ƙaiƙayi da kuma fitar ruwan da ya saɓawa al’ada daga gaban mace. Yoni kalma ce ta yaren Sanskrit da ke nufin al’aurar mace kuma yin wannan abun, wanda aka fi sani da turara gaban mace , na nufin mace ta tsuguna a saman kwanon tafasasshen ruwan maganin gargajiya. Tabon jiki na iya samuwa a gaban mace bayan an ji ciwo, wanda hakan kan faru yayin haihuwa. Zai iya sa gaban mace ya ƙanƙance . Ƙaiƙayin gaba da kuma fitar ruwa wanda ba bisa al’ada ba ƙwayar cuta ke haddasa shi . (A kula: Yayin da ake nufin gaban mace da al’aura gaba ɗaya, amma ana magana ne akan bututun da ke haɗa savis da bolba ko al’aurar ta da ake iya gani) Mun zanta da masana magunguna don bincika ko turara gaban mace na sawaƙe waɗannan lalurori. Babu hujja a kimiyance A cewar Makarantar magunguna ta Harvard da ke Amurka babu wata hujja a kimiyance da ta goyi bayan turara gaba. Kwalejin mata da lalurar masu juna biyu ta Amurka , hukuma ce ta ƙwararru a Amurka ta shaidawa Africa Check cewa bata bada shawarar a turara gaba. Ta ce: Bama ma bada shawarar a yi wani abu a gaban haka kawai, hakan zai iya jawo matsala. Dr Tshi Nakanyane, wanda aka fi sani da Dr Naks , amintaccen likitan mata da masu lalurar juna biyu ne da ke aiki a asibitin Steve Biko Academic Hospital a Pretoria. Ya ce shima bai san wata hujja da ta goyi bayan wannan da’awar ba. Turaren zai iya yin illa fiye da taimakawa. Zai iya ƙona ya kuma takurawa ma’aunin ph na gaban wanda zai iya ƙarawa gaban barazanar sake samun ƙwayar cuta, Nakanyane yayi gargaɗi akai. Hukumar Kimiyya ta Biritaniya bata bada shawarar a turara gaba don tsaftace shi ba. Ta bada shawarwari na kai tsaye ta yadda gaban mace zai kasance cikin tsafta da lafiya. Ta ce: Abu ne mai kyau a guji saka sabulai masu ƙanshi, jel ko maganin kashe ƙwayar cuta don zasu iya taɓa kwayar bakteriya mara illa da ma’aunin ph na gaban, su kuma hargitsa gaban. Ayi amfani da sabulun da bashi da ƙanshi don wanke kewayen gaban a hankali kullum. Gaban zai tsaftace kansa ta ciki da ruwan da gaban ke fitarwa na al’ada. A tuntuɓi likita idan an samu rauni a gaba, ƙaiƙayi ko fitar ruwa. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url